Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen shugabannin APC na tsagin Ganduje da Shekarau a Kano

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen shugabannin APC na tsagin Ganduje da Shekarau a Kano

  • Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin rushe shugabannin jam'iyyar APC na Kano tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje
  • Kotun ta jadadda cewa tsakanin Sanata Ibrahim Shekarau da suka zabi Harun Zago a matsayin shugabansu na halatattun shugabanni
  • Kotun ta ce tsagin na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba su yi zabuka a matakin mazaba da kananan hukumomi

Abuja - Wata babban kotu mai zamanta a Abuja karkashin Mai Shari'a Hamza Mua'zu ta soke dukkan shugabannin jam'iyyar All Nigeria Peoples Congress da ke biyayya ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Da ya ke yanke hukuncin a ranar Talata, alkalin ya amince ce bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ne halatattun zababun shugabanni, Daily Nigerian ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen shugabannin APC na tsagin Ganduje da Shekarau a Kano
Kotu ta rushe zaben shugabannin APC na tsagin Ganduje, ta tabbatar da hallarcin tsagin Shekarau. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce tsagin Gwamna Ganduje ba su yi zabe a matakin mazabu ba da kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu na rushe zaɓen ɓangarensa

Abdullahi Abbas ne ke jagorantar tsagin Ganduje yayin da Ahmadu Haruna Zago ke jagorantar tsagin Shekarau.

Wadanda suka shigar da karar sune Muntaka Bala Sulyman da mambobin jam'iyyar su 17,980 yayin da wadanda aka yi kararsu kuma sun hada da APC, Mai Mala Buni, Shugaban Riko, John Akpanudoedehe, da hukumar INEC.

Lauyoyin wadanda suka shigar da karar shine Nuraini Jimoh, SAN, wadanda kuma suke kara wadanda aka yi kara su ne Sule Usman, SAN da Mashood Alabelewe.

Idan za a iya tuna wa, an yi zabuka biyu a Kano, inda Abdullahi Abbas ya zama shugaban tsagin Ganduje yayin da shi kuma Abdullahi Haruna Zago ya zama shugaban tsagin Shekarau.

Bayan zaben, tsagin Shekarau ta shigar da kara gaban kotu.

Kwamitin sauraron korafi na kasa ta APC ta ce Abbas ne shugaba halattace

Kara karanta wannan

2023: Duk ‘Dan shekara 60 ya hakura da neman mulki – CNYF ta ba Atiku, Tinubu jan-kati

A bangare guda, kwamitin sauraron korafi da uwar jam'iyyar APC ta kafa ta yi na'am da zaben Abbas a matsayin halastaccen shugaban APC a jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da ya ke nuna kin amincewarsa da hukuncin da kwamitin da aka kafa karkashin Dr Tony Macfoy ta zartar, Haruna Zago ya ce:

"Hedkwatar jam'iyyar APC na kasa bata riga ta amince da kowa a matsayin shugaba ba, amma za ta yi hakan idan ranar ya zo kuma za ta bada satifiket ga ainihin zababbun shugabannin APC.
"Ba ni kadai na yi zaben ba; wasu 'yan takarar uku sun fafata da ni, ba kamar nasu ba inda Abbas kadai ya yi takara. Ba matsalar; Idan mun kai gadan, Allah ya nuna mana yadda za mu tsallake ta."

Rikicin APC a Kano: Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu na rushe zaɓen ɓangarensa

Babban kotu da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta rushe zaben shugabannin jam'iyyar APC na bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ranar Litinin zamu dawo da Sabis jihar Zamfara, Matawalle

Bangarorin biyu sun yi zabuka biyu a ranar 18 ga watan Oktoba amma uwar jam'iyyar ta amince da zaben da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi.

Bangaren Sanata Ibrahim Shekarau sun zabi Haruna Dan Zago a matsayin shugaban su yayin da bangaren Ganduje suka zabi Abdullahi Abbas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164