Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul'aziz Yari, da Sanata Marafa sun yi magana kan shirin ficewa daga APC
- Rahotannin da mutane ke yaɗuwa sun nuna cewa Yari da Sanata Marafa sun koma PDP bayan ganawa da Saraki a Kaduna
- Jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun fito sun yi karyat kan zargin ficewa daga APC da ya fara yawo a kafafen sada zumunta
- Sanata Marafa yace babu dalilin da zai sa wasu tsirarun mutane masu kudirin boye sun fitar da su daga APC
Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari, da tsohon sanata daga jihar, Sanata Kabiru Marafa sun musanta rahoton cewa sun koma PDP.
Premium Times tace a ranar Asabar mutane sun yaɗa a kafafen sada zumunta cewa mutanen biyu sun fice daga APC kuma sun koma PDP.
Jita-Jitar ta bayyana cewa jiga-jigan APC biyu sun gana da tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, a wani biki a Kaduna.
Yari ya musanta rahoton
Kakakin tsohon gwamna Yari, Ibrahim Muhammad, kuma tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, yace wannan ƙagaggen labari ne kawai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma kara da cewa makiyan tsohon gwamnan Zamfara a siyasa ne suka kirkiri labarin domin cimma wata manufa ta su.
Sanata Marafa ya yi karin haske
A nasa ɓangaren, da yake musanta rahoton a wata sanarwa da ya fitar, Kabir Marafa, ya kira jitar-jitar da, "Tunanin wasu tsiraru dake bakin cikin cigaba da ganin su a APC."
Marafa ya musanta maganar cewa shi da Yari zasu koma PDP biyo bayan ganawa da Sanata Bukola Saraki.
Punch ta rahoto Tsohon sanatan yace:
"Kundin ƙasar nan ya bamu damar ganawa, halarta, tattaunawa da kuma zuwa duk inda muke so tare da wanda muke so. Dagaske ne mun je Kaduna ɗaura auren diyar Sheikh Bala Lau, shin hakan laifi ne?"
"Lokacin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya halarci ɗaura auren ɗan shugaban kasa Buhari, shin hakan ya nuna zai koma APC?"
"Da mu aka gina APC har ta zo matakin da take a yanzun, saboda haka ba zai yuwu wani ya yaɗa jita-jitar da zata sa mu saki aikin da muka fara ga wasu mutane ba."
Yari da Marafa ba su jin daɗin rashin adalcin da ake kokarin yi a jagorancin APC na jihar Zamfara tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle.
A wani labarin kuma Maganar Gwamna El-Rufa'i na rokon yan Najeriya kada su zabi PDP a 2023 ya bar baya da kura
Gwamnan Kaduna ya roki yan Najeriya musamman mutanen jihar kada su kuskura su zabi jam'iyyar PDP a 2023.
Sai dai wannan magana ba tai wa yan Najeriya dadi ba, inda tuni wasu suka fara sukar gwamnan.
Asali: Legit.ng