Gwamnan Nasarawa: APC bata shirya faduwa a 2023 ba, muna da shiri mai kyau
- Gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana shirin jam'iyyar APC na ci gaba da mulki a zaben 2023 Mai zuwa
- Gwamnan na jihar Nasarawa ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Laraba
- Ya kuma shaida cewa, yana daga shirin jam'iyyar APC su ci gaba da mulki wannan yasa suke taka-tsantsan akan komai
Nasarawa - Gabanin zaben 2023, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce shirin jam’iyyar APC mai mulki shi ne ta san yadda zata yi nasara a zaben.
Gwamna Sule, wanda ya kasance bako a shirin Politics Today na Channels Tv a jiya Laraba, ya ce jam’iyyar na taka-tsantsan wajen gudanar da taronta da kuma zabar manyan jami’an da za su gudanar da harkokinta.
A cewarsa:
“Shirin mu ba shine mu fadi zabe a 2023 ba kuma duk abin da muke yi kenan.
“Don haka ne ma muke taka-tsan-tsan a majalisa, muna taka-tsantsan wajen zabar jami’an jam'iyyar na kasa, muna taka-tsantsan wajen yanke hukunci.
“Maimakon tada jijiyar wuya, abin da ya kamata duk wadanda ke son wannan mulki su yi shi ne su gabatar da kansu a matsayin mutane masu gaskiya, kwararrun mutane wadanda ke da ikon karbar mulki daga hannun Muhammadu Buhari tare da gina abin da ya fara.”
Ya Batun takarar su Tinubu da Osinbajo?
Gwamnan ya kuma yi magana game da rade-radin da ake ta yadawa na aniyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da dai sauransu kan tsayawa takara.
Yayin da yake bayyana cewa masu neman shugabancin kasar nan sun bunkasa kwarewarsu a fannin shugabanci domin ya gaji shugaba Buhari a 2023, ya ci gaba da cewa dole ne su tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa suna da dukkan abin da ya kamata wajen jagorantar kasar.
A cewarsa, ‘yan Najeriya ne za su tantance wanda zai gaji Buhari.
A cewarsa:
"Kowane daya daga cikinsu zai iya shiga ya iya nunawa jama'a don su goyi bayansa. A karshen wannan dai, 'yan Najeriya ne ke iya yin hakan (su zaba).
"Da zarar kun sami damar gamsar da 'yan Najeriya cewa wannan shi ne abin da ya dace, mutane suna da damar kwatantawa su a ce wannan shi ne mutumin da ya dace."
Duk da cewa har yanzu ba a tantance takamaiman ranar ba, amma kwanan baya shugaba Buhari ya amince da watan Fabrairun 2022 ga jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta na kasa, kamar yadda The Nation ta rahoto.
APC ta ba Buhari wuka da nama na tsayar da lokacin gudanar taron gangami
A wani labarin, gwamnonin jam’iyyar APC sun nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai tantance lokacin da taron gangamin jam’iyyar zai gudana.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnonin karkashin kungiyar Progressive Governors’ Forum (PGF) sun bayyana hakan a daren Lahadi, 21 ga watan Nuwamba a Abuja bayan sun gudanar da wani muhimmin taro na bayan fage.
Kusan gwamnonin APC 20 ne suka halarci taron wanda aka gudanar a dakin taro na gidan Gwamnonin Jihar Kebbi da ke Asokoro Abuja da misalin karfe 9:20 na dare.
Asali: Legit.ng