Shugaba Buhari ya tsayar da lokacin da za a yi taron gangamin APC na kasa
- Bayan da jam'iyyar PDP ta gudanar da taron gangaminta, jam'iyyar APC ma ta bayyana lokacin da za ta yi nata
- A yau Litinin ne gwamnonin APC suka gana da shugaba Buhari, inda suka amince da watan Fabrairu a matsayin watan taron gangamin
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan ganawar sirri da gwamnonin APC suka yi jiya Lahadi a Abuja
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar da za ta gudanar da babban taronta na gangami a watan Fabrairu, 2022, The Nation ta ruwaito.
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PGF Gwamna Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Bagudu ya gana da shugaban kasa da shugaban kwamitin rikon kwarya Mai Mala Buni da takwaransa na Jigawa Mohammed Badaru.
Ganawar da Gwamnonin APC, an yi ta ne bayan ganawar sirri da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaba Buhari ne ke da ta cewa
A tun farko, gwamnonin jam’iyyar APC sun nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai tantance lokacin da taron gangamin jam’iyyar zai gudana.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnonin karkashin kungiyar Progressive Governors’ Forum (PGF) sun bayyana hakan a daren Lahadi, 21 ga watan Nuwamba a Abuja bayan sun gudanar da wani muhimmin taro na bayan fage.
Kusan gwamnonin APC 20 ne suka halarci taron wanda aka gudanar a dakin taro na gidan Gwamnonin Jihar Kebbi da ke Asokoro Abuja da misalin karfe 9:20 na dare.
Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri a Abuja
A baya kun ji cewa, Gwamnanonin jihohin Najeriya dake jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun shiga ganawar sirri a gidan ajiya bakin Gwamnan jihar Kebbi dake Abuja, ranar Lahadi, 21 ga Nuwamba 2021.
Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi sun ce zaman bai rasa nasaba da lamarin taron gangamin jam'iyyar da ake shirin yi. Wadanda ke hallare a tarin sun hada da Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; da Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.
Asali: Legit.ng