Sanata Walid Jibril: Za mu fatattaki jam'iyyar APC a 2023

Sanata Walid Jibril: Za mu fatattaki jam'iyyar APC a 2023

  • Tsohon sanata kuma shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Walid Jibril, ya ce babbar jam’iyyar adawa za ta fatattaki APC a zaben 2023
  • Ya yi wannan furucin ne a wurin liyafar daurin auren dan shugaban kungiyar teloli da masu harkokin sutturun Najeriya, NUTGTWN, John Adaji
  • Jibrin ya ce akwai alamun hakan ya tabbata sakamakon yadda harkokin tsaron kasar nan su ke kara tabarbarewa don haka ‘yan Najeriya da dama za su juya wa APC baya

Tsohon sanata kuma shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Walid Jibril, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta sa APC ta kwashe komatsanta a zaben 2023, The Nation ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a liyafar daurin auren dan shugaban kungiyar tailoli da masu harkokin suttura a Najeriya ta NUTGTWN, John Adeji.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana sirri, ya ce Buhari na goyon bayan shugaba daga yankin Igbo

Sanata Walid Jibril: Za mu fatattaki jam'iyyar APC a 2023
Za mu fatattaki jam'iyyar APC a 2023, Walid Jibril. Hoto: The Nation
Asali: UGC

The Nation ta ruwaito yadda shugaban ya kula da yadda kullum rashin tsaro ya ke yawaita a kasar nan kuma ya ce PDP za ta jajirce wurin kawo gyara, don haka ‘yan Najeriya da dama za su juya wa APC baya.

Dama yayin jawabi a ranar masana’antun nahiyar Afirka wacce majalisar dinkin duniya ta tanadar don farfado da masana’antu a Afirka, John Adaji ya ce:

“Muna bukatar gwamnatin da zata jajirce wurin samar da masana’antu a Najeriya.”

Walid ya bayyana cewa idan PDP ta gabatar da dan takararta kuma ta bayyana yankin da ta dauko shi, APC za ta sauka daga kujerar mulki.

Ya ce PDP a shirye take da ta bunkasa ma’aikatu a Najeriya

Kamar yadda ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ba Buhari shawara ya yi watsi da kudirin da Majalisa za ta kawo gabansa

“Mu ‘yan PDP muna da kula da jajircewa akan bunkasa masana’antu a Najeriya.
“Mun tattauna kuma mun amince akan lallai shugaban jam’iyyar mu ya kasance daga arewa ta tsakiya. Kuma an tabbatar da wannan.
“Sauran shirye-shirye kuma su na kan hanya. Kwanannan za mu tattauna akan yankin da ya kamata mu zabo dan takarar shugaban kasarmu.”

Ya kara da bayyana yadda su ke da yakinin wani shugaban kasan da zai mulki Najeriya ya kasance dan jam’iyyar PDP.

Kuma zai jajirce wurin kawo karshen rashin tsaro don maido da Najeriya halin kwanciyar hankali jama’a su ci gaba da walwala.

Rashin tsaro ya yawaita a Najeriya

A cewar Jibrin, saboda tsabar rashin tsaron da ke kasar nan, kowa ya san halin da ake ciki. Don haka shugaba jajirtacce ne kadai zai kawo karshen wadannan matsaloli.

Ya kara da bayyana yadda PDP za ta tsaya tsayin-daka wurin bubbugo da masana’antu don jama’a su samu wurin ayyuka kuma kasa samu ci gaba.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164