Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja
- Babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya shiga labule tare da tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, a Abuja
- Shugabannin biyu sun yi ganawar ne a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba a gidan Kalu
- Ana zaton ganawar tasu ba zata rasa nasaba da hada-hadar siyasa kan wanda zai gaji shugaba Buhari a 2023 ba
Abuja - Jagoran jam’iyyar All Progessives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na cikin wata ganawa da tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, a Abuja.
Jaridar Punch ta rahotio cewa Tinubu ya isa gidan Kalu da karfe 4:25 na yammacin yau Asabar, 20 ga watan Nuwamba.
Yan siyasar sun rungume junansu tare da yin gaishe-gaishe a tsakaninsu.
An tattaro cewa bayan gaisawar sai suka shiga cikin ganawar sirri.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta yi bayanin cewa kafin ganawar sirrin, Kalu ya yi godiya ga Allah a kan warkwar Tinubu cikin sauri.
Tinubu ya dawo Najeriya a ranar 8 ga watan Oktoba, bayan ya shafe wasu watanni a Landan, inda aka yi masa aiki a gwiwa.
Zuwa yanzu ba a san dalilin ganawar tasu ba amma ana ganin ba zai rasa nasaba da wasu ci gaba na siyasa da tattalin arziki a kasar ba.
Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin shugabannin biyu na hararar kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Su dukkaninsu sun kasance tsoffin gwamnonin jihohinsu daga 1999 zuwa 2007.
2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari
A wani labarin, mun ji cewa akalla sarakunan gargajiya sama da 300 daga kudu maso yamma ne ke goyon bayan takarar tsohon gwamnan jihar Lagas, Sanata Bola Tinubu, a zaben shugaban kasa na 2023.
Sanata Dayo Adeyeye, shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu ne ya bayyana hakan a Gbongan, jihar Osun, rahoton Punch.
Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kungiyar mai suna ‘South West Agenda for Asiwaju for 2023’ a mazabar Irewole.
Asali: Legit.ng