Da duminsa: Soludo ya magantu bayan lashe zaben Anambra

Da duminsa: Soludo ya magantu bayan lashe zaben Anambra

  • Zababben gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo ya mika godiyarsa ga Ubangiji kan nasarar da ya samu a zaben da ya lashe
  • Soludo ya bayyana cewa, shekaru 12 kenan da ya dinga neman kujerar sakamakon goyon baya da ya ke samu daga jama'a masu son ya shugabance su
  • Ya ce wannan nasarar ba tashi kadai ba ce, nasara ce ga jama'ar jihar Anambra da suka fito kwansu da kwarkwatarsu wurin zabensa

Anambra - Farfesa Charles Chukwuma Soludo, zababben gwamnan jihar Anambra, ya yi martani kan nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar da aka kammala.

Baturiyar zaben Anambra, Farfesa Florence Obi a ranar Laraba, ta bayyana Soludo a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben bayan samun kuri'u 112,229 a zaben.

Da duminsa: Soludo ya magantu bayan lashe zaben Anambra
Da duminsa: Soludo ya magantu bayan lashe zaben Anambra. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jim kadan bayan ayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben, zababben gwamnan ya yi jawabi ga manema labarai daga garinsu na Isuofia.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Dalilai 5 da suka sa PDP ta sha mummunan kaye a zaben gwamna

Dan takarar APGAn ya mika godiyarsa ga jama'ar Anambra da suka zabe shi. Ya mika godiyarsa ga jam'iyyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga cikakken jawabin Soludo:

"Cike da kankan da kai tare da mika godiya ga Ubangiji, na amince da sakamakon zaben gwamnan Anambra na 2021 kamar yadda INEC ta sanar.
"Wannan ya bayyana iko tare da karfin izzar Ubangiji tare da jajircewa da kokarin jama'a.
"A tsawon shekaru 12 tun da mutane suke goyon bayan mu bauta musu, mun jajajirce har zuwa wannan lokacin.
"Wannan lokacin ya zo kuma Godiya da yabo sun tabbata ga Ubangiji. Akwai jerin mutanen da Ubangiji yayi amfani da su wurin cikar wannan burin.
"Da farko akwai godiya da nake mika wa ga mambobin jam'iyyar APGA, ballantana jigon jam'iyyar na kasa, Gwamna Willie Obiano da matarsa, shugaban jam'iyya na kasa, Victor Oye da matarsa.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

"'Yan majalisar yardaddun jam'iyyar, mambobin NEC da suaransu kan yadda suka bani damar takara karkashin jam'iyyar. Godiya mai tarin yawa kwamitin kamfen, masu ruwa da tsaki da suaransu"

Wasu jami'an INEC sun kauracewa zaben Ihiala a Anambra

A wani labari na daban, wasu jami'an wucin-gadi na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da aka tura karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun kauracewa rumfunan zabensu saboda matsalar tsaro.

A ranar Asabar da ta gabata, ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala saboda matsalar tsaro, Daily Trust ta wallafa.

A yayin bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba, Farfesa Comfort Obi, baturiyar zaben jihar, ta ce hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, ba ta tura kayayyakin zabe ba saboda rahoton halin da ake ciki da ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng