2023: Abin da jam'iyyar PDP za ta yi idan APC ta tsayar da Jonathan matsayin ɗan takara, Tambuwal

2023: Abin da jam'iyyar PDP za ta yi idan APC ta tsayar da Jonathan matsayin ɗan takara, Tambuwal

  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana abin da PDP za ta yi idan APC ta tsayar da tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi mata takarar shugaban kasa a 2023
  • Tambuwal yayin wata hira da aka yi da shi ya yi magana kan rashin hallartar babban taron PDP na kasa da tsohon shugaban kasa Jonathan bai yi ba
  • Gwamnan wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya yi hasashen cewa akwai alamun Jonathan ya iya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Sokoto - A baya-bayan nan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa tana shirin tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar ta a 2023, amma har yanzu ana tattaunawa kan batun.

Gwamnan na jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya kuma bayyana dalilan da yasa tsohon shugaban kasa Jonathan bai hallarci babban taron jam'iyyar PDP na kasa ba da aka yi kwanan nan.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Anambra: Dan takaran APGA ya ce dan takaran APC mai garkuwa da mutane ne

A cewar Tambuwal, Jonathan yana da wani taron da zai hallarta a kasar Kenya, don haka jam'iyyar ta bashi izini ya tafi.

2023: Abin da zamu yi idan jam'iyyar APC ta tsayar da tsohon shugaban kasa Jonathan, Tambuwal
2023: Abin da zamu yi idan jam'iyyar APC ta tsayar da tsohon shugaban kasa Jonathan, Tambuwal. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Depositphotos

A hirar da ya yi da Premium Times, gwamnan wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya ce:

"Da farko, Obasanjo ya dena siyasar jam'iyya lokaci mai tsawo, a shekarar 2014. Shugaban kwamitin shirya taron tare da gwamnonin Bayelsa, da na Oyo, wanda shine sakatare sun tuntubi Jonathan. Sun same shi sun nuna masa tsare-tsaren taron. Ya nemi uzuri cewa yana hanyarsa ne na zuwa taron AU, taron kasa da kasa da za a yi a Kenya. Ba zai yiwu ya hallarci wuri biyu a lokaci guda ba kuma mun fahimta."

Tambuwal wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin an yi taron cikin nasara kuma yana aiki da takwarorinsa don karfafa jam'iyyar gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo

Kazalika, Tambuwal, tsohon kakakin majalisar dattawa, ya kuma yi tsokaci kan hasashe da ake yi na yiwuwar Jonathan ya sauya sheka zuwa APC.

Dan siyasan na Nigeria ya ce labarin har yanzu jita-jita ne amma ya bukaci Jonathan kada ya sake ya koma jam'iyyar adawar domin zai iya karewar tamkar Adams Oshiomhole da Ize-Iyamu.

Tambuwal ya ce:

"A cewar jita-jita, nima wai ina shirin komawa jam'iyyar APC amma jita-jita ne. Na yi wata hira da VON Hausa inda aka yi min tambaya mai kama da wannan kan yiwuwar Jonathan ya koma APC. Muna bashi shawara kada ya yi tunanin yin hakan. Idan ba haka ba, ta yaya za su tallata shi? Lamarinsa zai zama tamkar na Adams Oshiomhole da Ize-Iyamu.
"Ka san a Edo, lokacin zaben gwamna na karshe, galibi abinda shi Adams ya ce game da dan takararsa, Ize-Iyamu, ne suka zama abin kamfen. Mutane za su binciko abubuwan da irin su Buhari, Tinubu da sauran jiga-jigan APC suka ce game da Jonathan. Ina tabbatar maka abinda za mu yi a PDP kenan. Don haka, ina shawartar Shugaba Jonathan, idan yana son takara, ya nema a PDP a maimakon tunanin zuwa APC."

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164