Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine

Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine

  • Dan takarar kujerar gwamnan Anambra karkashin inuwar PDP, Valentine Ozigbo, yace har yanzun bai cire ran samun nasara ba
  • Zaɓen wanda hukumar INEC ta bayyana a matsayin wanda bai kammalu ba, za'a ƙarisa shi ne ranar Talata
  • Ozigbo ya yi kira ga mutanen da ba su kaɗa kuri'un su ba, su fito ranar Talata domin zaɓen jam'iyyarsa ta PDP

Anambra - Ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Anambra. Valentine Ozigbo, yace har yanzun yana sa ran shi zai lashe zaben da za'a ƙarasa ranar Talata.

Dailytrust ta rahoto cewa hukumar zabe INEC ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, kasancewar ba'a gudanar da zaɓe a ƙaramar hukumar Ihiala ba.

Valentine Ozigbo
Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A halin yanzu, Farfesa Chukwuma Soludo, na jam'iyyar APGA, shine ke kan gaba da kuri'u mafi rinjaye bayan lashe 18 daga cikin kananan hukumomi 20.

Kara karanta wannan

Shugaban jam'iyyar APGA da ta lallasa APC, PDP a zaben Gwamnan Anambra ya magantu

Duk da cewa Ozigbo shike mara masa baya a yawan kuri'u, ya lashe zaɓe a karamar hukuma ɗaya ne kacal.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai sauran magana a gaba - Ozigbo

Da yake zantawa da manema labarai kan zaben da za'a ƙarasa, Ozigbo yace har yanzun faɗan bai ƙare ba, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A cewarsa, har yanzun akwai kuri'u sama da 248,000 dake ƙasa a ƙaramar hukumar Ihiala da sauran inda ba'a yi zaɓen ba.

Akwai masu kaɗa kuri'a 148,407 a ƙaramar hukumar Ihiala kaɗai, inda INEC ta tabbatar da ba'a gudanar da zaɓe ba.

Ku fito ku zabi jam'iyyar PDP

A jawabinsa, Ozigbo ya yi kira ga mutane su fito domin jefa wa jam'iyyarsa ta PDP kuri'un su.

Sai dai ya koka kan rawan da siyan kuri'u ya taka a zaben, wanda ya bayyana a babbar matsalar da aka samu.

Kara karanta wannan

Dan takarar PDP, Ozigbo ya lallasa Farfesa Soludo a karamar hukumar Ogbaru, Anambra

Yace:

"Muna kira ga INEC ta gudanar da zabe a duk inda ba su jefa kuri'a ba, domin mutane sun fito kwansu da kwarkwata amma aka hana su damar su."

A wani labarin kuma Gwamnan APC ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Gwamnan Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya sallami ciyamomi 21 da kuma kansiloli dake faɗin jiharsa.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis, gwamnan ya gode wa ciyamomin bisa aikin da suka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262