Zaben Anambara: Takaitaccen tarihin zaben gwamna tun shekarar 1999 zuwa bana

Zaben Anambara: Takaitaccen tarihin zaben gwamna tun shekarar 1999 zuwa bana

A ranar 6 ga watan Nuwamba jihar Anambra ta kada kuri'a domin zaben sabon gwamna. Kamar yadda aka saba, kamar duk zabukan da aka yi a jihar, wannan zabe na musamman yana da sabon salo.

A cikin wannan rahoto, Legit.ng ta kawo muku takaitaccen tarihin zaben gwamna a jihar Anambra.

Jihar Anambara: Takaitaccen tarihin zaben gwamna tun 1999, da yadda ya sauya a Anambra
Zabe a jihar Anambra | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

A ranar 29 ga Mayun 1999, aka rantsar da Chinwoke Mbadinuju a matsayin gwamnan farar hula na jihar Anambra.

A ranar 26 ga watan Mayun 2003 ne aka rantsar da Chris Ngige a matsayin sabon gwamnan jihar, amma aka cire shi a watan Maris na shekarar 2006 bayan Peter Obi na jam’iyyar APGA ya shigar da kara a kansa kan zargin tafka magudi a zabe.

A nasa bangaren, wani bangare na Majalisar Dokokin Jihar Anambra, ya tsige Obi a ranar 2 ga Nuwamba, 2006, aka maye gurbinsa da Virginia Etiaba, mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Dalilai 5 da suka sa PDP ta sha mummunan kaye a zaben gwamna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar 9 ga watan Fabrairun 2007, Misis Etiaba ta mika mulki ga Obi bayan da kotun daukaka kara ta soke tsige shi.

A ranar 14 ga Afrilu, 2007, an zabi Andy Uba na PDP a matsayin sabon gwamnan jihar kuma a ranar 29 ga Mayu, an rantsar da shi.

A ranar 14 ga watan Yunin 2007 ne kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa wa’adin Peter Obi bai kare ba; don haka babu gurbi a kujerar gwamna. Hakan yasa aka tsige Andy Uba daga mukaminsa tare da maye gurbinsa da Obi.

A ranar 6 ga Fabrairun 2010, Peter Obi ya sake zama gwamna a karo na biyu na tsawon shekaru hudu, bayan zazzafar hamayya da Chris Ngige.

An rantsar da Cif Willie Obiano a ranar 17 ga Maris 2014 bayan ya lashe zaben ranar 16 ga Nuwamba 2013.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

An rantsar da Gwamna Willie Obiano na jam’iyyar APGA a wa’adi na biyu a ranar 17 ga Maris 2018.

Yanzu kuma an kada kuri'u a zaben gwamnan Anambra na shekarar 2021, wanda sakamakon zabe daga hukumar INEC ya bayyana Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda ya lashe zabe.

Zuwa yanzu INEC ta karbi sakamakon zaben kananan hukumomi 19 cikin 21

A wani labarin, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da karbar sakamakon zaben kananan hukumomi 19 na jihar daga cikin 21, The Nation ta ruwaito.

Sauran biyun kuma a cewar Hukumar ana dakon su kuma za su isa Hukumar da ranar yau din nan.

Mista Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa, mai kula da kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ne ya sanar da hakan da safiyar Lahadi a ofishin hukumar da ke Awka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.