Rikici ya barke yayin da 'yan majalisa 6 suka tsige kakakin majalisar Imo

Rikici ya barke yayin da 'yan majalisa 6 suka tsige kakakin majalisar Imo

  • 'Yan majalisar dokokin jihar Imo sun tsige kakakin majalisa biyo bayan sabanin da ya gindaya a tsakani
  • Rahoto ya bayyana cewa, wasu 'yan majalisu 19 ne suka fito cikin jerin wadanda suka zabi a tsige kakakin
  • A bangare guda, an ce wani mataimakin kakakin majalisar da aka tsige shi ne ya shigo da wasu 'yan majalisu shida aka tube kakakin

Imo - A safiyar Litinin ne ‘yan majalisar dokokin Imo suka tsige kakakin majalisar dokokin jihar, Paul Emeziem.

The Nation ta ruwaito cewa, Sun maye gurbinsa da wani Kennedy Ibe.

An gudanar da aikin ne a cikin tsauraran matakan tsaro inda ‘yan majalisar 19 daga cikin 27 aka ce sun rattaba hannu kan takardar tsigewar.

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin da 'yan majalisa suka tsige kakakin majalisar Imo
Taswirar jihar Imo | Hoto: thenationonlinenf.net
Asali: UGC

An tattaro cewa mataimakin kakakin majalisar, Amara Iwuanyanwu da ake zargin an tsige shi ne ya mamaye zauren majalisar tare da ‘yan majalisa shida da wasu jami’an tsaro domin tsige shugaban majalisar.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa Farfesa Shehu Dalhatu na Jami'ar BUK rasuwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaman wanda bai wuce mintuna 15 ba ya zo karshe, wanda nan take Ibeh ya karbi mukamin sabon shugaban majalisar.

Rahoto daga jaridar Punch ya bayyana cewa, wasu 'yan majalisu shida ne suka kitsa tsige shugaban majalisar, wanda ya jawo rikici.

Sabon shugaban majalisar dai na daya daga cikin ‘yan majalisa 18 da suka rattaba hannu a kan kudirin tsigewar, inda suka tsige tsohon mataimakin shugaban majalisar.

Bayan tsige kakakin majalisar Filato, an tsige mataimakin kakakin majalisar Imo

A wani labarin, jaridar Punch ta ruwaito cewa, an tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Amara Iwuanyanwu.

An cire shi ne karkashin tsauraran matakan tsaro yayin zaman majalisar a ranar Talata 2 ga watan Nuwamba.

Ekene Nnodim, mai wakiltar mazabar Orlu, ya gabatar da kudiri mai dauke da sa hannun ‘yan majalisa 18 daga cikin 27 na tsige Iwuanyanwu a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar zaman kan karar da Sheikh Zakzaky ya shigar kan Gwamnatin tarayya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.