Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a zaben gwamnan Anambra na 2021
Mabiyanmu su sani, akwai 'yan takara 18 ne suke fatan maye gurbin Gwamna Willie Obiano.
Daga cikinsu akwai:
Charles Soludo - APGA Senator
Andy Uba - APC
Valentine Ozigbo- PDP
Sanata Ifeanyi Ubah - YPP
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana, akwai akwatuna 1,820 da za su karba masu kada kuri'a 846,994 a mazabar Anambra ta arewa.
A mazabar Anambra ta tsakiya, za a samu akwatunan zabe 3,987 wadanda za su karba masu kada kuri'a 887,295 da suka yi rijista.
A Anambra ta kudu, za a samu akwatunan zabe 1,934 domin masu kada kuri'a 794,203.
Jimillar masu kada kuri'a da suka yi rijista sun kama 2.52 miliyan. Su ne za su fitar da makomar dan takarar da zai shugabanci jihar a shekaru hudu masu zuwa.
Legit.ng na nan daram a Anambra domin kawo muku bayanai kan yadda zaben ke tafiya. Ku kasance tare da mu!
Za a ci gaba da kada kuri'a a rana ta biyu na zaben gwamnan Anambra
A yau ne za a baiwa masu kada kuri'u da suka cancanta damar kada kuri’unsu a zaben gwamnan jihar Anambra, saboda matsalolin fasaha da gazawar tsarin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta samu.
Sabanin fargabar tashe-tashen hankula a gabanin zaben, an samu fitowar masu kada kuri'a a ko'ina kuma an gudanar da zabe cikin lumana, Vanguard ta ruwaito.
Sai dai malan zabe ba su isa kan lokaci a rumfunan zabe da dama ba, kuma amincewar da INEC ta baiwa masu kada kuri’a ta hanyar tsarin tantance masu kada kuri’a, BVAS, ya fuskanci koma baya a rumfunan zabe da dama a fadin jihar.
Biyo bayan korafin da wasu ‘yan takara da manyan ‘yan siyasa suka yi, INEC ta tsawaita kada kuri’a har zuwa ranar Lahadi.
An kuma tsawaita atisayen fiye da lokacin rufewa da karfe 2:30 na yammacin jiya Asabar.
Kwamishinan zabe na INEC a jihar Anambra, Dokta Nkwachukwu Orji, ya ce BVAS ta gaza a fannoni da dama saboda matsalar manhaja da aka samu.
A cewarsa, saboda haka an kara wa’adin ne domin a baiwa wadanda ba su samu damar kada kuri’unsu yin hakan.
Rukunan zabe da yawa sun fuskanci kutse, wanda hakan ya jinkirta tsarin jefa kuri'a da jin takaicin daga masu jefa kuri'a.
Sama da mutum 2,500 basu kada kuri'a ba a kauyen Ezinifite Okpuno
A rumfa ta 8 da ke kauyen Ezinifite Okpuno, karamar hukumar Awka ta kudu, sama da mutum 2,500 basu kada kuri'a ba.
Daga cikin mutum 3,072 da suka yi rijista, mutum 150 kacal suka kada kuri'a.
An fara kirgen kuri'u
An fara kirgen kuri'u a Amawbia Ward 1, PU 10
Hukumar INEC ta kara lokacin kada kuri'a sakamakon matsalar da aka samu da na'urar BVAS
Kwamishanan INEC na jihar Anambra ya sanar da dage lokacin rufe kada kuri'a zuwa karfe 4 na yamma sakamakon matsalolin da aka fuskanta da na'urar BVAS a wurare daban-daban.
Kwamishanan, Dr Nkwachukwu Orji, ya sanar da hakan ne ga manema labarai a hedkwatan INEC dake Awka.
Ya bayyana cewa akwai yiwuwan a cigaba da zaben har zuwa gobe/
An yi awon gaba da wani dan sanda wanda ya bugu da giya kafin zuwa rumfar zabe
Bayan jama'a sun yi korafi kan yadda wani jami'in dan sanda wanda ya debi barasa kafin zuwa rumfar zabe keyi, an yi awon gaba da shi.
Shugabanci nagari muke so, cewar tsohon mai shekaru 70 da aka tantance
Peter Akpati, tsohon mai shekaru 70 ne da aka tantance domin kada kuri'a a rumfar zabe ta 9 da ke gundumar Agu Awka.
A yayin zantawa da Legit.ng, Akpati ya ce: "Jama'a su fito su kada kuri'a, babu amfanin tsoro. Akwai isasshen tsaro.
"Muna bukatar shugabanci nagari a Anambra kuma hakan ne kadai zai taimaka mana wurin zaben wanda muke so."
Tsohuwa mai shekaru 70 ta cire tsoro ta fito kada kuri’a
Wata ‘yar shekara 70 mai suna Catherine Egbuche, wacce ta kasance gurguwa ta fito domin kada kuri’a a rumfar zabe ta Amaubia Primary School, Amawbia, jihar Anambra.
Da take zantawa da Legit.ng, Catherine ta ce ta fito domin shiga tsarin zaben duk da cewar har yanzu bata samu kudin sallamarta ba a matsayinta na ‘yar fansho.
A karshe Soludo ya isa rumfar zabe
Dan takarar jam'iyyar APGA Charles Soludo ya isa rumfar zabensa don kada kuri'a.
Yanzu kusan karfe 12:30 amma ba mu fara zabe ba," in ji Soludo.
Dan takarar na APGA ya ce zai sake jawabi ga manema labarai bayan ya kada kuri'arsa cikin nasara.
Dan takarar APC Andy Uba ya kada kuri’a, ya ce babu abun da zai hana shi lashe zabe
Dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan jihar Anambra, Sanata Andy Uba ya kada kuri'arsa.
Legit.ng ta rahoto cewa yayin da yake jawabi bayan kada kuri'a, Uba ya ce an riga an gama zabe yayin da ya nuna yakinin cewa zai lashe zaben.
Ya ce:
"Komai na tafiya daidai. Ta kare ma APGA, babu inda PDP za ta je."
Dan takara Ozigbo ya yi jawabi bayan kada kuri'a
Bayan kada kuri'a, dan takarar PDP, Valentine Ozigbo ya ce ya yi matukar farin ciki ganin yawan jama'a da suka fito zaben.
"A gaskiya na ji dadin ganin abinda ke faruwa a yankin Amezi. Na ga masu zaben sun fito sosai," yace.
Ozigbo ya yi korafin cewa an yi jinkiri kafin fara zaben.
"Ban ji dadi da lamarin ya dade ba a fara ba," yace.
Dan takarar PDP ya ce an samu matsalar sabis a yayin da masu kada kuri'a suka taru.
Jami'an tsaro sun mamaye rumfunan zabe a Awka
Jami'an tsaro sun mamaye rumfunan zabe da ke Akwa, a jihar Anambra
Dan takaran jam'iyyar, Valentine ya dira rumfar zabensa don kada kuri'a
Dan takaran jam'iyyar, Valentine Ozigbo, tare da iyalinsa sun dira rumfar zabensa dake Social Centre, Amesi, karamar hukumar Aguata don kada kuri'arsu.
Gwamna Willie Obiano da matarsa sun kada kuri’a
Gwamna Willie Obiano da matarsa, Ebelechukwu sun kada kuri’arsu a rumfar zabe ta Eri Primary school, PU 004, Otuocha 1, Aguleri, karamar hukumar Anambra ta gabas da misalin karfe 9:28 na safe.
Gwamnan wanda ya zanta da manema labarai jin kadan bayan kada kuri’arsa ya ce:
“Na bukaci mutanen Anambra da su fito su yi zabe. Ko ina akwai zaman lafiya. Ku fito ku yi zabe.”
Masu kada kuri'a sun balle zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumi zabe
Masu kada kuri'a a gunduma ta 9 da ke Ezimezi a Amawbia, karamar hukumar Awka ta kudu, sun balle zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumin fuska saka kuri'a.
Masu zaben sun dinga tururuwar fitowa tun wurin karfe 8:30 amma sai aka ce su koma gida tare da sako takunkumin fuska, Punch ta wallafa.
Wannan lamarin ne yasa tsohon dan majalisar jihar Anambra, Chikodi Aghanya ya kwatanta lamarin da 'shirme'
Na'urar BVAS ta mazabar Soludo ba ta aiki
Masu kada kuri'a sun fusata. Kamar yadda suka ce, na'urar BVA ba ta aiki a mazabar dan takarar Charles Soludo.
"Babu abinda ke aiki a nan, ga katin zabe na," wani mai kada kuri'a ya sanar da Arise News TV.
Mazabar Sanata Andy Uba
Har yanzu jami'an INEC ba su iso mazabar Andy Uba ba, kamar yadda Arise TV ta wallafa
An fara kada kuri’a a zaben gwamnan Anambra na 2021
Da misalin karfe 8:30 na safe, an fara kada kuri’a a rumfar zaben PU005, Umudioka, karamar hukumar Dunukofia da rumfar zabe ta Area 13, Ichida 1, karamar hukumar Anaocha.
Rumfar zabe: Eri Primary school, PU 004
Rumfar zabe: Eri Primary school, PU 004, Otuocha 1, Aguleri, karamar hukumar Anambra ta gabas.
Har zuwa karfe 8:00 na safe, jami’an INEC suna nan suna shirye-shirye, sannan akwai masu jefa kuri’u yan kadan da ke duba sunayensu.
A wannan rumfa ne Gwamna Willie Obiano zai kada kuri’arsa.
Rumfar zabe: PU001 – Kindergarten Primary School, Obuofu 1
Rumfar zabe: PU001 – Kindergarten Primary School, Obuofu 1, Ward 05, Abagana III, karamar hukumar Njikoka.
A PU001, jami’an INEC na nan suna manna sunayen masu zabe da aka yi wa rijista, da kuma kafa rumfar zabe.
Zuwa yanzu masu jefa kuri’u uku sun hallara. Gaba daya an yi wa mutane 516 rijista, a bisa rahoton The Cable.
Dan takaran jam'iyyar AAC, Chidozie Nwankwo ya janye daga takarar zaben gwamnan Anambra
Dan takara jam'iyyar jam'iyyar African Action Congress AAC, Chidozie Nwankwo, ya janye daga takarar kujeran gwamnan jihar Anambra.
Nwankwo ya sanar da cewa dukkan wadanda sukayi niyyar zabensa yanzu kawai su goyi bayan dan takaran jam'iyyar PDP, Valentine Ozigbo.
Rahoto BBC
Ba za a yi zabe ba a rumfunan zabe 86, in ji INEC
Yayin da yan Anambra ke shirin zabe, a lura cewa hukumar INEC ta bayyana a baya cewa ba za a yi zabe ba a rumfuna 86 cikin rumfunar zabe 5,720 da ke jihar saboda basu da masu jefa kuri'u.
An yi gyara a tsarin tsaro
Sufeto Janar na yan sandan, IGP Alkali Usman Baba ya cire mataimakin Sufeto Janar na yan sandan, DIG Joseph Egbunike a matsayin shugaban tawagar tsaro na zaben gwamnan Anambra yan sa’o’I kafin zaben.
Kakakin rundunar yan sandan kasar, CP Frank Mba, ya tabbatar da cewar an sauyawa DIG Egbuike wurin aiki, amma bai bayyana dalilin cire babban jami’in wanda ya kasance dan asalin jihar Anambra ba.
Sai dai kuma, kakakin shiyar, Princess Nkeiruka Nwode, ta ce DIG Egbunike bai yi murabus ba kamar yadda aka rahoto a wasu bangarori.
Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng
Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng