Shugaban kasa a 2023: Matasan arewa sun nuna goyon bayansu ga shahararren dan siyasar kudu
- Kungiyar matasan arewa ta nuna goyon bayanta ga bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu domin ya karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
- A cewar kungiyar, Kalu na da gogewa da cancantar da ake bukata domin jagorantar kasar
- Ta yi kira ga jam'iyyar APC da ta tsayar da tsohon gwamnan a matsayin dan takara daya tilo a babban zaben kasar mai zuwa
Birnin tarayya, Abuja - Wata kungiya ta matasan arewa karkashin inuwar Arewa Youths for Orji Uzor Kalu ta nuna goyon bayanta ga bulaliyar majalisar dattawa, domin zama shugaban kasa na gaba.
Kungiyar ta bayyana matsayinta ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa dauke da sa hannun jagoranta na kasa, Yakubu Muhammad; mukaddashin sakatarenta, Abdulkadir Muhammad; sakataren shirye-shirye, Ibrahim Abdullahi, da kuma daraktan labaranta, Musa Waziri.
A cikin sanarwar da aka fitar a Abuja a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, sun bayyana Kalu a matsayin wanda ya fi cancanta da zama shugaban kasa a babban zaben 2023.
Kungiyar ta kuma bukaci jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da ta fara shirin tsayar da shi a matsayin dan takara daya tilo, rahoton Punch.
Sanarwar ta zo kamar haka:
“Kwarewar Kalu da gogewarsa sun sa ya fi kowa cancanta don shugabantar Najeriya a 2023.
“Wannan na iya zama abun mamaki ga ‘yan Najeriya musamman wadanda ke da muradin tsayawa takarar kujera ta daya a kasar.
“Saboda haka, karbuwar da Sanata Orji Uzor Kalu ya samu ya nuna hukuncin da matasan jihohin Arewa 19 suka yanke na mara masa baya domin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
"Kalu shugaba ne na hakika wanda ke da tarihin da ke nuna cewa zai iya dorawa a kan tarin nasarorin da gwamnati mai ci ta samu.
"Kalu ne ya fi dacewa da APC a 2023. Ya kasance dan takarar shugaban kasa wanda ke da gogewa a ma'aikata mai zaman kanta, da kuma bangaren zartarwa da dokoki na gwamnati.
“Ya zama wajibi a bayyana cewa, yayin da ‘yan Najeriya ke neman Shugaban kasa daga yankin Kudu maso Gabas, masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC ba su da bukatar su kara zurfafa bincike saboda Orji Uzor Kalu mutum ne mara kabilanci, shi ne dan takarar da ya dace a jam’iyyar.
"Tasirinsa ya karade dukkanin yankuna shida na kasar.
"Ya kasance shugaban hukumar ruwa ta Borno a lokacin da yake da shekaru 25; ya yi shugabancin kamfanoni da dama sannan kuma ya yi gwamnan jihar Abia.
"Mun yarda cewa abun da Najeriya ke bukata a yanzu shine jajirtaccen shugaba wanda zai iya kula da kasa kamar Najeriya. Wannan mutumin shine Kalu."
Matasan arewa sun saki jerin sunayen yan siyasan da za su marawa baya don zama Shugaban kasa a 2023
A wani labarin, gabannin zaben Shugaban kasa na 2023, wata kungiya a arewa, mai suna Northern Youth Leaders Forum (NYLF), ta bayyana sunayen yan siyasan da suke tunanin marawa baya don hayewa kujerar.
Kwamrad Elliot Afiyo, Shugaban kungiyar na kasa, shi ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Sun.
A cewar rahoton, Afiyo ya ce kungiyar za ta duba yiwuwar marawa yan takarar Shugaban kasa a 2023 daga kudu da arewa maso gabas baya.
Asali: Legit.ng