Matasan arewa sun saki jerin sunayen yan siyasan da za su marawa baya don zama Shugaban kasa a 2023
Gabannin zaben Shugaban kasa na 2023, wata kungiya a arewa, mai suna Northern Youth Leaders Forum (NYLF), ta bayyana sunayen yan siyasan da suke tunanin marawa baya don hayewa kujerar.
Kwamrad Elliot Afiyo, Shugaban kungiyar na kasa, shi ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Sun.
A cewar rahoton, Afiyo ya ce kungiyar za ta duba yiwuwar marawa yan takarar Shugaban kasa a 2023 daga kudu da arewa maso gabas baya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Buba Marwa a matsayin Shugaban NDLEA
Legit.ng ta lissafo jerin sunayen yan siyasan da kungiyar tace za ta duba yiwuwar marawa baya a zaben Shugaban kasa na gaba:
1. Atiku Abubakar
2. Bala Mohammed
3. Bola Tinubu
4. Nyesom Wike
5. Orji Uzor Kalu
6. Peter Obi
Afiyo ya ce babu adalci kuma baa bun yarda bane wani ya fito daga arewa maso yamma yace zai yi takarar Shugaban kasa a 2023.
Ya ce yankin ya samar da Shugaban kasa biyu da mataimakin Shugaban kasa.
Yiwuwar duba abokin takara
Kungiyar matasan arewar ta kuma yi magana game da yiwuwar duba abokin takara wajen marawa Shugaban kasa baya.
Arewa maso gabas
Bala Mohammed
Atiku Abubakar
Danjuma Goje
Farfesa Babagana Zulum
Ahmad Lawan
A hada su da kowanne dan siyasan kudu da aka lissafo a kasa:
1. Nyesom Wike
2. Ifeanyi Okowa
3. Ben Ayade
4. Raymond Dokpesi
5. Peter Obi
6. Rochas Okorocha
7. Orji Kalu
Kudu maso yamma
1. Bola Tinubu
2. Kayode Fayemi
3. Yemi Osinbajo.
A hada su da
1. Nasir El-Rufai
2. Abdullahi Ganduje
3. Simon Lalong
4. Atiku Bagudu
5. Babandende
KU KARANTA KUMA: Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji
A wani labarin, sohon gwamnan jihar Kano kuma Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar zabe (INEC) mai ci, Sanata Kabiru Gaya ya nuna muradinsa na son ganin yankin kudancin kasar ta samar da Shugaban kasar Najeriya na gaba.
Sanatan mai wakiltan Kano kudu ya bayyana cewa idan shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas a 2023, zai zama rashin adalci idan arewa ta nemi kujerar Shugaban kasar kuma.
Ya yi martanin ne a wata hira da jaridar Daily Sun wanda aka wallafa a ranar Asabar, 16 ga watan Janairu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng