Gwamna El-Rufa'i ya rantsar da sabbin Ciyamomi 21 da suka lashe zaɓe a fadin jihar Kaduna

Gwamna El-Rufa'i ya rantsar da sabbin Ciyamomi 21 da suka lashe zaɓe a fadin jihar Kaduna

  • Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi da aka zaɓa a faɗin jihar
  • Ya roki ciyamomin daga kowace jam'iyya da su saka tsoron Allah a zuciyoyin su, kuma su yi wa al'ummar su adalci
  • Daga cikin waɗan da suka samu nasara a zaɓen, jam'iyyar APC ta samu kujeru 16, yayin da PDP ke da 5

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya roƙi sabbin ciyamomi da mutane suka zaɓa su maida hankali wajen yi wa al'ummarsu aikin da suke bukata.

Gwamnan ya kuma taya sabbin shugabannin murna bisa nasarar da suka samu a zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar.

El-Rufa'i ya yi wannan magana ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, wanda ke kunshe da jawabinsa a wurin rantsar da ciyamomin.

Kara karanta wannan

A yi wa yan bindiga Afuwa kuma a ware kuɗaɗen ɗaukar nauyinsu, Sheikh Gumi ya magantu

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i
Gwamna El-Rufa'i ya rantsar da sabbin Ciyamomi 21 da suke lashe zaɓe a fadin jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufa'i FB Fage
Asali: Facebook

Wanda ke bada mulki ne ya baku - El-Rufa'i

A jawabinsa gwamnan Kaduna yace:

"Allah SWT, wanda yake bada mulki ga wanda yaso, shine ya zaɓe ku, kuma ya mika muku amanar mutanen yankunan ku, ba tare da duba addini ko ƙabila ba."
"A madadin gwamnatin Kaduna, ina taya ku murnar samun nasara, kuma ina muku fatan samun nasara wajen sauke nauyin al'ummar ku."

Hakanan gwamnan ya kuma gargaɗe su, kada su sake su nuna banbanci tsakanin waɗan da suka zaɓe su, da waɗan da ba su zaɓe su ba.

Wane mataki gwamnati ta ɗauka na gyara?

Bugu da ƙari gwamnan ya bayyana cewa tuni gwamnatinsa ta fara ɗaukar matakan inganta ayyukan ƙananan hukumominta ga al'umma.

A cewarsa daga cikin abubuwan da ta fara, akwai magance rashin isassun ma'aikata ta hanyar bada umarnin ɗaukar injiniyoyi, lauyoyi, da masu zane-zane domin aiki a kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

Ya sakamakon zaɓen ya kasance?

Sakamakon zaɓen da aka gudanar, ya nuna cewa jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta samu kujerun ciyamomi guda 16.

Yayin da abokiyar hamayyar ta, PDP ta samu kujeru 5, amma ba'a gudanar da zaɓe a karamar hukumar Birnin Gwari ba saboda matsalar tsaro yayin da sakamakon Jaba yake gaban kotu.

Mulkin soja ya fi na APC walwala

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnan Benuwai yace Mafi munin mulkin soja da aka taba yi a Najeriya yafi gwamnatin Buhari walwala da jin daɗi

A cewar gwamna Ortom ya karanta tarihin mulkin Najeriya, har da na soja, wanda ake cewa duk lalacewar mulkin farar hula ya fi na soja.

Yace a yanzun ta sauya zani, domin shi bai taba gani ko jin labari na wani mulki kamar na yanzin karkashin jam'iyyar APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262