Da Dumi-Dumi: Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, In ji Kwankwaso

Da Dumi-Dumi: Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, In ji Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bai gamsu da ayyukan da gwamnatin Kano karkashin Ganduje ke yi ba
  • Jagorar tafiyar ta Kwankwasiyya ya bayyana rashin jin dadinsa bisa basusuka da Ganduje ke karbowa don yin ayyukan da ya ke ganin basu zama dole ba
  • Kwankwaso ya ce ba shi da wata matsala da shi Gandujen kansa sai dai ayyukansa ne sun kaucewa tsarin abin da al'ummar Kano ke bukata

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce bai gamsu da ayyukan da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi ba a jihar.

Kwankwason ya bayyana gakan ne yayin da aka yi hira da shi a ARISE Television a safiyar ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da Dumi-Dumi: Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, In ji Kwankwaso
Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, Kwankwaso. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya ce duk da cewa ba shi da wata matsala tsakaninsa da Ganduje, amma bai gamsu da irin ayyukan da ya yi ba.

Kara karanta wannan

Ina gwamna ban taba karbo bashin ko kwandala daya ba, Kwankwaso ya sake caccakar Ganduje

A kan alakarsa da gwamnan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babu wata matsala tsakaninsu, kawai dai maganan aiki ne tabbas ba mu gamsu da abin da gwamnati ke yi ba.
"Watakila wannan shine tushen matsalar da aka fara samu bayan an zabe shi. Akwai wasu abubuwa da suke yi da ya saba wa tsarin mu da kuma irin tunaninmu."

The Cable ta rahoto cewa Kwankwaso ya yi wannan furucin ne a lokacin da wasu masu nazarin siyasa ke ganin akwai yiwuwar ya shirya da Gandujen.

Ganduje ya jinjinawa Kwankwaso cikin sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwarsa da makon da ta gabata.

Gwamnan ya ce yana daraja alakar da ke tsakaninsu tsawon shekaru da kuma alaka ta aiki da siyasa.

A baya dai aminan juna ne a siyasance tsawon shekaru.

Sai dai, alakarsu ta fara samun matsala ne jim kadan bayan Ganduje ya gaji Kwankwaso a matsayin gwamnan Kano a shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu

Ban taba karbo bashin ko kwandala ba lokacin ina gwamna, Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yace lokacin da yake gwamna na tsawon shekara 8 bai taba karbo bashin ko naira ɗaya ba.

Ya kuma zargi Gwamnan Kano na yanzu, Dakta Abdullahi Ganduje, da jefa jihar cikin ƙaƙani kayin bashi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Kwankwaso, wanda shine shugaban tafiyar Kwankwasiyya, yace mafi yawan ayyukan da gwamnan ke yi da kuɗaɗen bashin sam ba su zama dole ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164