Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

  • Dr Obiora Okonkwo, dan takarar gwamna na jam'iyyar ZLP a zaben Anambra na watan Nuwamba ya zubar da hawaye
  • Okonkwo ya sharbi kuka ne a garin Okpoko a yayin da ya tafi kaddamar da aikin titi ya ga wata mata mai goyo ta fada cikin kwata
  • Daga bisani an gano cewar matar tana cikin mawuyacin hali hakan yasa gidauniyar Okonkwo ta taimaka mata da N200,000

Anambra - Dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

CBN ta magantu kan dalilin bacewar manhajar e-Naira a intanet, yaushe kuma za ta dawo

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra
Dan takarar gwamna ya zubar da hwaye yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matar, Amarachi Nwachukwu tana hanyar zuwa siyo pure water ne da ta ke siyarwa domin ciyar da iyalanta kuma goye da yarta a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ta ke bawa manema labarai halin da ta ke ciki, Nwachukwu ta ce:

"Na karbi bashin N200 ne daga wani domin in siyo pure water da zan siyar domin in ciyar da 'ya'ya na saboda mun shafe kwanaki biyu ba mu ci abinci ba. Ina hanyar zuwa shagon ne nayi tuntube na fadi."

Matar ta taki sa'a yayin da Okonkwo, shugaban United Nigeria Airlines, ta hannun gidauniyarsa ya bata kyautar N200,000 domin ta fara sana'a da za ta kula da iyalinta.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

Mutanen Anambra na cikin mawuyacin hali, Okonkwo

Da ya ke magana, dan takarar na ZLP ya ce mutanen jihar suna shan bakar wahala saboda gazawar gwamnati wurin kulawa da bukatun mutanen.

Ya ce:

"Mun ga wata mata ta fadi, watakila saboda yunwa kuma mun siya mata abinci. Da muka gano ba za ta iya cin abincin da kanta ba, mun bata abinci da jinjirinta. Mun kuma tallafa mata da N200,000 ta hannun gidauniya ta domin ta fara sana'a."

Ya cigaba da kokawa kan mawuyacin halin da mutanen jiharsa ke ciki a karkashin gwamnatin APGA yana mai cewa shekaru 16 ya isa su sauya rayuwar mutane a jihar.

Da ya ke martani kan sabon aikin titin, shugaban unguwa, Francis Enemuo ya ce Allah ne ya aiko musu dan kasuwar kuma yana addu'ar Allah ya bashi nasara domin ya tallafawa mutanen jihar.

Wani dan majalisa ya koma jam'iyyar PDP ana saura kwana 11 zabe a Anambra

Kara karanta wannan

Jerin tituna 21 da za su ci makudan kudade, kuma gwamnatin Buhari ta amince a yi

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyya APGA a jihar Anambra ta rasa mutanenta duk sun sauya shekarsu, baya ga ‘yan majalisar jihar har da mataimakin gwamnan jihar, Nkem Okeke.

Premium Times ta ruwaito yadda Chukwuka Ezenwune, dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Idemili ta kudu ya koma PDP daga jam’iyyar APGA.

Ezenwune ya bayyana sauya shekar ta sa ne a ranar Talata bisa ruwayar Premium Times.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164