Wani dan majalisa ya koma jam'iyyar PDP ana saura kwana 11 zabe a Anambra
- Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta rasa ‘yan majalisa 6, duk sun koma jam’iyyar APC
- Har mataimakin gwamnan jihar Nkem Okeke ma ya tsere zuwa jam’iyyar ta PDP mai mulki a jihar
- A ranar Talata wani dan majalisar jihar, Chukwuka Ezenwune ya sauya sheka ana saura kwana 11 zabe
Anambra -Jam’iyya APGA a jihar Anambra ta na ta rasa mutanen ta duk su na sauya shekar su, baya ga ‘yan majalisar jihar har da mataimakin gwamnan jihar, Nkem Okeke.
Premium Times ta ruwaito yadda Chukwuka Ezenwune, dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Idemili ta kudu ya koma PDP daga jam’iyyar APGA.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ezenwune ya bayyana sauya shekar ta sa ne a ranar Talata bisa ruwayar Premium Times.
Dan majalisar ya ce sanadin sauya shekar ta sa shi ne rashin iya siyasa da kuma karfa-karfa da wasu mutane su ke yi a cikin jam’iyyar.
A cewar sa, a 2012 yadda jam’iyyar ta fara girma, an yi tunanin APGA za ta kara karfi ta mamaye kasa baki daya ba samar da gwamna a jihar Anambra kadai ba, amma yanzu ci baya take yi.
Ezenwune ya ce ya ji kunyar ayyukan da mazabar sa ta kaddamar idan aka kalli yawan kudin da gwamnatin tarayya ta ware wa gwamnatin jihar a cikin shekaru 7 da su ka shude.
Ya ce:
“Na yi farin cikin shiga jam’iyyar PDP, cike ta ke da tsari kuma an gina ta fiye da tunanin mutum.
“Ba zan iya nuna wani aiki ba a karamar hukuma ta baya ga wanda na yi matsayin aikin mazaba ta.
Ya cigaba da cewa:
“A wancan taron jam’iyyar ta yi, an ware ni da mabiya na, don haka na gane ba ni da wani abu da zan yi a APGA bisa wannan dalili na nemi shawarar mutane na.
“Na taimaka wurin gina jam’iyyar nan saboda na shiga ne ba don ta zama jam’iyyar inyamurai ba, kamar yadda su ke nuna wa mutane."
Dama APGA ta rasa ‘yan majalisa 6 na jihar Anambra kuma duk sun koma APC, cikin su har da mataimakin gwamnan jihar, Nkem Okeke.
Asali: Legit.ng