Rikici ya barke a jam'iyya bayan dakatar da shugabanta da sakatarensa

Rikici ya barke a jam'iyya bayan dakatar da shugabanta da sakatarensa

  • Kwamitin Aiki na Jam’iyyar SDP ya amince da dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar Anambra da sakatarensa
  • Sanarwar tana kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Shehu Musa Gabam, sakataren jam’iyyar SDP na kasa
  • Shugabannin biyu, jam'iyyar SDP ta zarge su da yi wa jam'iyyar zagon kasa kwanaki 14 gabanin zaben gwamnan jihar

Shugabancin jam'iyyar SDP na kasa ya amince da dakatar da Wester Okonkwo da Kay Anyachor, shugaba da kuma sakataren jam'iyyar reshen jihar Anambra.

Daily Trust ta ruwaito cewa an dakatar da mutanen biyu ne bisa zargin “cin dunduniyar da jam’iyyar” kwanaki kadan ga zaben gwamnan jihar Anambra.

Shehu Musa Gabam, sakataren jam’iyyar SDP na kasa a wata wasika ya bayyana cewa Okonkwo da Anyachor sun nuna rashin biyayya da rashin iya hada kan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa

Rikici ya barke a fitacciyar jam'iyya bayan dakatar da shugabanta da sakatarensa
Alamar jam'iyyar SDP | Hoto: hausa.leadership.ng
Asali: UGC

Gabam ya ce Kwamitin Aiki na Kasa na jam'iyyar (NWC) ya amince da dakatar da su daga ofis daidai da doka ta 19.4 da 6 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar na 2018 wanda aka yiwa kwaskwarima, The Sun ta kara da cewa.

An umurci mutanen biyu da su mika mukamansu ga mataimakansu nan da nan kafin a ci gaba da bincike da kuma yanke hukunci a jam'iyyar.

Duk da haka, Okonkwo a martanin dakatarwar, ya ayyana cewa shi ne shugaban SDP na jihar Anambra na ainihi.

Shugaban da aka dakatar ya dage cewa an zabe shi ne ta hanyar taron gangamin jiha, ya kara da cewa ba za a iya cire shi ba sai da mutanen da suka zabe shi.

Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18

Kara karanta wannan

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

Yayin da ake jiran zaben, ana sauran wata daya daidai da zaben gwamnan jihar Anambra, hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta (INEC) ta saki sunayen yan takaran zaben na karshe.

Legit.ng ta tattaro cewa a wannan jerin sunaye na karshe, hukumar ta sanya sunan Valentine Chineto Ozigbo matsayin dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Zaku tuna cewa a jerin sunayen da INEC ta saki a baya, jam'iyar PDP bata da dan takara saboda rikice-rikicen kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.