Labari da Hotuna: Kada ka sadaukar da rayuwarka kan yan sayasa, Gwamna ya halarci bikin ɗan abokin hamayyarsa
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya gargaɗi yan Najeriya a kan mutuwa kan yan siyasa
- Gwamnan wanda ya jima basu ga maciji da tsohon gwamnan Ekiti, Fayose, ya halarci bikin ɗan babban abokin faɗansa
- Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, gwamnan Ribas, Nyesom Wike da sauran manyan yan siyasa sun halarci bikin
Ekiti - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Mekinde, ya gargaɗi yan Najeriya kada su kuskura su siyar da ransu a kan wani ɗan siyasa a Najeriya.
Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a wurin bikin ɗan babban abokin hamayyarsa kuma tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose.
Dailytrust ta rahoto cewa duk da banbancin da suke da shi a siyasance, Makinde yana ɗaya daga cikin manyan baki a wurin ɗaura auren.
Gwamna Makinde da kuma Fayose sun jima basu ga maciji kan wanda zai jagoranci jam'iyyar PDP a yankin kudu maso yamma.
Su wa suka halarci bikin?
Hakanan kuma daga cikin waɗanda suka halarci bikin harda gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, wanda tsohon abokin adawar Fayose ne a siyasa.
Da kuma tsohon gwaman Eikiti, Olusegun Oni, wanda ya rasa tikitin takarar zarcewa a matsayin gwamna a hannun Fayemi.
Kun gani a zahiri - Mekinde
Da yake jawabi a wurin bikin, wanda ya samu halartar jiga-jigan siyasar Najeriya da suka haɗa da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, Makinde yace:
"Idan kuka duba tsofaffin gwamnonin Ekiti, Segun Oni da Fayose, ga kuma gwamnan yanzun, Fayemi, duk sun jagoranci jihar amma basu cikin jam'iyya ɗaya."
"Saboda haka duk waɗanda ke ganin zasu iya sadaukar da rayuwarsu a kan mu yan siyasa, su gaggauta canza tunani.
"Siyasa ba abu bane da zai sanadiyyar wani ya rasa ransa ba, muna fuskantar lokacin siyasa, shiyasa nake son gargaɗinku baki ɗaya."
Ba maganar rikicin addini
Gwamnan ya kara da cewa duk masu son tada rikicin addini to su sake tunani domin kuwa akwai auratayya tsakanin addinai, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
"Idan kuka duba Amarya da Ango, sun fito daga addinin kirista da Musulunci. Don haka masu rikicin addini ku sake tunani."
A wani labarin na daban kuma kun ji yadda Wani babban malami ya ɗirkawa budurwa cikin shege daga zuwa neman addu'a
Malamin dai ya amsa laifinsa da farko, amma daga baya ya musanta tuhumar da ake masa, amma ya amince zai ɗauki nauyin mai cikin.
A cewarsa bayan ta haihu ne za'a iya sanin gaskiyar waye uban jaririn ta hanyar kwajin kwayar halitta.
Asali: Legit.ng