Ni ne zan iya gyara Najeriya: Atiku ya bayyana irin kwarewarsa a shugabanci

Ni ne zan iya gyara Najeriya: Atiku ya bayyana irin kwarewarsa a shugabanci

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakr, ya bayyana iyawarsa a mulkin Najeriya
  • Ya bayyana cewa, shi ne zai iya gyara Najeriya ta samu ci gaba mai kyau da ake bukata
  • Ya kuma bayyana cewa, Najeriya na bukatar shugaba irinsa matukar ana son kasar ta ci gaba

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce Najeriya na bukatar shugabanci wanda zai gyara tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba a Abuja yayin gabatar da lacca na cika shekaru 70 da gabatar da littafin Shugaban Kamfanin DAAR Communications Plc, Cif Raymond Dokpesi.

Ya kara da cewa kasar na kuma bukatar jagora wanda zai hada kai, sake fasali da tabbatar da tsaron 'yan kasar.

Kara karanta wannan

2023: 'Ku sani babu rumfar zabe a kafafen sada zumunta' - YPP ta shawarci matasan Najeriya

Ni ne zan iya gyara Najeriya: Atiku ya bayyana irin kwarewarsa a shugabanci
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar | Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019 ya ce shi ne mutumin da ya dace da zai ba kasar abin da take bukata.

Da aka tambaye shi ko shi ne mutumin da ya dace kuma kasar ke bukata domin dawo da martabarta, sai ya ce:

“Na fadi hakan a baya, zan yi.
"Najeriya na bukatar shugabanci wanda zai iya hada kan kasar, ya kawo kwanciyar hankali, sake fasali da sake fasalin tattalin arzikin da zai kawo tsaro."

Dokpesi ya yi kira ga matasa da su kare dimokradiyya su hada kai don kowa ci gaba a kasar.

Shahararren dan jarida, wanda kuma ya kaddamar da littafinsa mai taken: “The handkerchief” don murnar cikarsa shekaru 70, ya bukaci matasa da su ci gaba da jajircewa wajen gina kasa mafi nagarta da ci gaba don mayar da ita wuri mafi kyau.

Kara karanta wannan

2023: Babban Fasto ya yi hasashen wanda zai karbi shugabanci daga hannun Buhari

Sai dai, gabanin babban taron gangamin jam'iyyar PDP, ana ci gaba da samun

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kwamitin tantancewa na jam'iyyar PDP ya hana 'yan takara uku tsayawa takarar mukamai a kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar.

Wadanda ba su cancanta ba da mukaman inji PDP sun hada da: Farfesa Wale Oladipo (Osun) wanda ya nuna sha’awarsa ga mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu.

Hakazalika da Okey Muo-Aroh (Anambra) wanda ya nuna sha’awar matsayin Sakataren Kasa Dakta Olafeso Eddy (Ondo) Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam'iyyar.

Rikici a APC yayin da aka rantsar da 'yan wani tsagi bayan taron gangami a Ribas

A bangare jam'iyyar APC mai mulki kuwa, rikicin da ya barke a cikin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya dauki wani sabon salo na daban.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa bangaren da ke biyayya ga Sanata Magnus Abe a ranar Talata 18 ga watan Oktoba, ya kaddamar da babban jami’in gudanarwar sa.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

A cewar rahoton, an yi bikin ne a Freedom House, sakatariyar yakin neman zaben da Sanata Abe ya kafa a GRA ta Fatakwal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.