2023: 'Ku sani babu rumfar zabe a kafafen sada zumunta' - YPP ta shawarci matasan Najeriya
- Jam'iyyar YPP ta shawarci matasan Najeriya a fadin kasar da su yi rijistar katin zabe domin samun irin shugabancin da suke muradi
- YPP ta tunatar da matasan cewa su sani babu rumfar zabe a kafafen sada zumunta
- Har ila yau, jam'iyyar ta yi kira ga ci gaba da neman zaman lafiya da hadin kan kasar
Kwara - Jam’iyyar Young Progressives Forum (YPP) reshen jihar Kwara ta yi kira ga matasa a fadin kasar da su yi rijistar katin zabe domin cimma irin shugabancin da suke muradi a kasar.
Jam’iyyar ta yi wannan kira ne jim kadan bayan gudanar da gangami a Ilorin, babban birnin jihar a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, shugaban kungiyar a jihar, Charles Folayan, ya bukaci matasan da su ci gaba da neman zaman lafiya da hadin kan kasar, Daily Trust ta rahoto.
“Ku tuna, babu rumfar zabe a shafukan zumunta. Idan har akwai adalci a kasar, kuri’unmu za su yi tasiri. Kuma kun san me? Mune mafi rinjaye!
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mu ci gaba da zaman lafiya da aiki don zaman lafiya da hadin kan Najeriya.”
Daily Post ta kuma rahoto cewa, Shugaban jam’iyyar ya ce koda dai matasa ne za su gaji kasar nan, ya zama dole su fara yi wa Najeriya hidima.
Ya ci gaba da bayyana cewa a bayyana yake cewa korafi a shafukan sada zumunta ko yin zanga-zanga a titi ba Za su magance matsalolin da kasar da ‘yan Najeriya ke fuskanta ba a yanzu.
Ya kara da cewa:
“Don haka, ya zama dole mu bar titi zuwa wurin zabe don cimma sauyin YPP.”
Ya bayyana cewa hanya daya da za a kawo sauyi a tsarin dimokradiyya da shugabanci.
Ya ce:
“Wannan shine manufar kafa YPP a matsayin jam’iyyar matasa wadanda suka shiga siyasa don yi wa Jama’a hidima, ba wai kansu ba.
“Ya kamata mu daina maimaita shugabanni wadanda ba za su kaimu ko’ina ba. Imma sun tsufa da yawa, basu da isasshen lafiya ko kuma sun gaji.”
Matasan Arewa sun nemi jam'iyyun siyasa su ba Tinubu tikitin shugabanci a 2023
A wani labarin, wata kungiyar Arewa mai suna Arewa Youth Alliance for 2023, ta bayyana goyon baya ga tsohon gwamnan jihar Legas kuma Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin mafi kyawun dan takarar shugaban kasa a 2023.
Kungiyar ta bukaci dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya da su fara shirin daukar Tinubu a matsayin dan takara daya tilo a Najeriya, Vanguard ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da aka ba manema labarai a ranar Laraba a Kano ta hannun Ko’odinetan kungiyar, Hon Bello Lawan Bello, ya ce:
“Shugaban jam’iyyar APC yana da gogewa, sanin kasa da makamar aiki, dabarun gudanarwa na jagoranci da hada kan Najeriya bisa nasarorin da ya samu a matsayinsa na Gwamnan Legas kuma jagoran APC na kasa tare da ba da gudummawa mai yawa ga nasarar gwamnatin Buhari."
Asali: Legit.ng