Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya fice daga cikin jam'iyyar, ya bayyana dalilai
- Wani babban jigon jam'iyyar APC a jihar Yobe, ya miƙa takardar ficewarsa daga cikin jam'iyyar kan wasu dalilii
- Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin APC a 2023, Alhaji Aji Kolomi, yace ya ɗauki wannan matakin ne a karan kansa
- A cewarsa duba da yanayin da jam'iyya ke ciki a yanzu, ya ga ya dace ya fice daga cikinta
Yobe - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Yobe ƙarƙashin APC, Alhaji Aji Kolomi, ya yi murabus daga jam'iyyar APC a hukumance, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
A wata wasiƙa da ya aike wa shugaban APC na gundumar Ngurbuwa, ƙaramar hukumar Gubja, jihar Yobe, Aji yace:
"Bayan girmama wa gareka, ina mai sanar da kai cewa na ɗauki matakin yin murabus daga jam'iyyar AOC bisa ratsin kaina."
"Ina miƙa godiya ta gare ka da sauran yan majalisar zartarwa bisa goyon bayan da kuka nuna mun lokacin neman takara ta a 2019, Nagode sosai."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa ya fita daga APC?
Mista Aji ya ƙara da cewa ya yanke wannan hukuncin ne a karan kansa da kuma yanayin tafiyar gwamnatin APC.
"Duba da yanayin siyasar dake faruwa a cikin jam'iyyar APC, daga yau Litinin 18 ga watan Oktoba na yi murabus daga APC, ga katin zama ɗan jam'iyya nan na haɗo da shi."
Shugabanni ku ji tsoron Allah - Aji
Tsohon jigon APC ya kuma roki shugabannin da aka zaɓa su saka Allah a ransu wajen sauke nauyin da al'umma ta ɗora musu.
A cewarsa za'a samu cigaba ne a mulkin demokaraɗiyya idan masu rike da madafun iko sun tabbatar da sauke nauyin dake kansu ba tare da nuna ban-banci ba.
Siyasar Kano: Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje
A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benuwai.
Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.
Asali: Legit.ng