Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC

Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC

  • Mataimakin shugaban PDP reshen jihar Yobe, tare da wasu manyan jiga-jigai sun koma jam'iyyar APC mai mulki
  • A cewar waɗanda suka sauya shekan, ba bu wani dalili da zai sa su cigaba da zama cikin PDP, saboda shugaban ƙasa na bukatar goyon baya
  • Gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba

Yobe - Wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar hammaya PDP reshen jihar Yobe, tare da mambobi sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Vanguard ta rahoto cewa daga cikin waɗanda suka koma APC har da, mataimakin shugaban PDP na jiha, Alhaji Usman Amale, da mataimakin sakatare, Malam Ahmadu Biriri.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito cewa gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, shine ya karbi masu sauya shekan ranar Talata a Damaturu.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jam'iyyar APC Ta Fitar da Sunayen Tawagar Kamfen 2023 Na Karshe, An Samu Sauyi

Gwamna Mala Buni
Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC Hoto: Mala Buni Social Media Team FB fage
Asali: Facebook

Gwamna Mai Mala Buni, wanda shine shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, ya nuna jin daɗinsa bisa matakin tsoffin jiga-jigan PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kun ɗauki matakin da ya dace - Buni

Gwamna Mai Mala Buni ya godewa mutanen bisa ɗaukar matakin shigowa APC domin bada gudummuwarsu wajen gyara Najeriya.

Gwamnan yace:

"A halin yanzu jam'iyyar APC ta maida hankali wajen haɗa kan Najeriya da kuma samar da cigaba ga yan ƙasa."
"A koda yaushe muna maraba da manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya daga kowane sashi, al'ada da kuma addinai."
"Hanyar warware matsalolin Najeriya ya dogara ne a kan siyasa, saboda haka ya zama wajibi mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen haɗa kawunan mu, domin cigaban ƙasar mu."

Ba zamu nuna muku banbanci ba

Gwamnan ya kuma tabbatar wa waɗanda suka shiga APC cewa babu maganar nuna bambanci tsakaninsu da sauran mambobin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan Goyon Bayan Gwamna APC, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Yuwuwar Wike Ya Fice PDP

A cewarsa APC zata baiwa kowane daga cikinsu damar shigowa a dama da shi, kamar yadda kowane mamban APC ke da ita, wajen kawo cigaba a Najeriya.

Meyasa suka koma APC?

Da yake jawabi a madadin masu sauya sheka, tsohon mataimakin shugaban PDP, yace babu wani dalili da zai sa su cigaba da zama a PDP.

"Ba mu da wani dalilin cigaba da zama a cikin PDP saboda shugaban ƙasar mu da kuma shugaban APC suna bukatar taimakon mu wajen gyara Najeriya."

A wani labarin kuma kun ji cewa Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Rahotanni sun nuna cewa mambobi sama da 5,000 ne suka koma APC a yankin karamar hukumar Ughelli, jihar Delta.

A cewarsu, sun ɗauki wannan matakin ne saboda gamsuwa da wakilcin mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Omo-Agage.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262