Jerin shugabannin PDP da aka yi a tarihi daga 1998 zuwa yanzu, da yadda ta kaya da su
- A Agustan 1998 wasu kwararrun ‘yan siyasa suka kafa jam’iyyar PDP a Najeriya
- Jam’iyyar PDP tayi shekaru 16 kan mulki, ta yi shugabanni na kasa 15 daga 1998
- Ekwueme, Ogbeh, Ali da Lar sun rike kujerar da ake sa rai Iyorchia Ayu zai dare
Nigeria - A shekaru 23 da kafuwar jam’iyyar PDP a Najeriya, ta yi shugabanni da-dama. Dr. Alex Ekwueme ne ya fara rike wannan kujera a matsayin rikon kwarya.
Legit.ng Hausa ta tattaro duk shugabannin jam’iyyar PDP na kasa da aka yi har zuwa Uche Secondus.
1. Dr. Alex Ekwueme
Dr. Ekwueme ne shugaban PDP na kasa na farko a tarihi, ya yi watanni uku rak a kan kujera sai ya yi murabus, ya shiga neman takarar shugaban kasa a zaben 1999.
2. Cif Solomon Lar
Marigayi Solomon Lar ya rike shugabancin PDP, kuma shi ne ya ba Olusegun Obasanjo tutar takara. Tsohon gwamnan ya sauka daga mukaminsa a karshen 1999.
3. Barnabas Gemade
A 1999 Barnabas Gemade ya doke Sunday Awoniyi wajen zama shugaban PDP na kasa. A wannan zabe ne aka fafata wajen takarar kujerar shugabancin jam’iyyar PDP.
4. Audu Ogbeh
Bayan Sanata Gemade ya sauka daga mukaminsa, sai Audu Ogbeh ya karbe shi. Shi ma Ogbeh ya yi murabus a 2005 a sakamakon sabaninsa da Olusegun Obasanjo.
5. Ahmadu Ali
Sai Kanal Ahmadu Ali wanda ya yi shekaru kusan hudu a kujerar da ya fara da matsayin shugaban riko. Tsohon Ministan ilmin ya na ofis daga 2005 zuwa 2008.
6. Prince Vincent Ogbulafor
A shekarar 2008 Prince Vincent Ogbulafor ya zama shugaban PDP bayan an gaza shawo kan manyan ‘yan takara na lokacin Sen. Anyim Pius Anyim da Dr. Sam Egwu.
7. Okwesileze Nwodo
Bayan saukar Ogbulafor sai abokinsa Dr. Okwesileze Nwodo ya gaje shi. Tsohon gwamnan na Enugu bai dadeba. Nwodo shi ne sakataren PDP na farko a 1998.
8. Haliru Mohammed
Rikicin da ya ci Nwodo ya yi sanadiyyar da Dr. Haliru Mohammed ya zama shugaban riko na PDP a 2010. Daga baya sai ya karbi mukamin Ministan sadarwa na tarayya.
9. Alhaji Kawu Baraje
Tsakanin shekarar 2011 zuwa 2012, Alhaji Kawu Baraje ne shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
10. Bamanga Tukur
Bamanga Tukur ya lashe zaben da aka yi na shugaban jam’iyya, ya shiga ofis a Maris, 2012. A lokacin Tukur ne PDP ta rasa jiga-jiganta daf da zaben 2015 da ta sha kashi.
11. Ahmad Adamu Muazu
Bayan an yi waje da Bamanga Tukur a 2014, sai aka maye gurbin shi da wani tsohon gwamna, Ahmad Adamu Muazu. Shi ma dai dole ya bar ofis bayan zaben 2015.
12. Ali Modu Sheriff
Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP
Ko da yanzu yana APC kamar wasu magabatansa, Sanata Ali Modu Sheriff ya rike shugabancin PDP har 2016. A lokacinsa ne PDP tayi ta fama da shari'a a gaban Alkali.
13. Ahmad Muhammad Makarfi
A 2016 jam’iyyar PDP tayi nasarar korar Ali Sheriff, Sanata Ahmad Makarfi wanda ya yi gwamna na shekaru takwas a jihar Kaduna ya zama shugaban riko na kasa.
14. Prince Uche Secondus
Bayan tafiyar Makarfi, sai Prince Uche Secondus ya zama shugaban jam’iyyar PDP a zaben 2017. Daga baya aka sauke shi, amma har yanzu maganar tana gaban kotu.
15. Iyorchia Ayu zai zama sabon shugaban PDP
Kwanakin baya ku ka ji jam'iyyar PDP ta yi ittifaki a kan wanda zai zama sabon shugabanta. An zabi Ayu Iyiorcha a matsayin magajin shugaba Prince Uche Secondus.
Sanata Ayu Iyiorcha ya taba rike mukamin shugaban majalisar dattawa na kasa. Ayu shi ne wanda aka zaba gabanin Ibrahim Shema da Sanata Nazifi Sulaiman
Asali: Legit.ng