Rikici a APC yayin da aka rantsar da 'yan wani tsagi bayan taron gangami a Ribas
- An rantsar da shugabannin jam'iyyar APC a jihar Ribas kwanaki kadan bayan gudanar da taron gangami
- Rahotanni sun bayyana cewa, an rantsar da 'yan tsagin Sanata Magnus Abe ne bayan zaben da aka yi
- An samu rabuwar kai a jam'iyyar APC yayin da aka yi taron gangami, inda aka samu bullar shugabanni biyu a wasu jihohin
Ribas - Rikicin da ya barke a cikin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya dauki wani sabon salo na daban.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa bangaren da ke biyayya ga Sanata Magnus Abe a ranar Talata 18 ga watan Oktoba, ya kaddamar da babban jami’in gudanarwar sa.
A cewar rahoton, an yi bikin ne a Freedom House, sakatariyar yakin neman zaben da Sanata Abe ya kafa a GRA ta Fatakwal.
Siyasar Kano: Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje
Jami'an sun hada da Golden Chioma a matsayin shugaban jam'iyya na jihar, Mike Amakiri, Mataimakin Shugaba, Inye Jack a matsayin Sakatare, da Joy Woko, shugabar matan jam'iyya a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da yake zantawa da manema labarai Chioma ya ce akwai majalisun unguwa, na kananan hukumomi da na jihohi da aka samar daga bangaren, sannan ya yi kira ga gwamna Nyesom Wike da ya shirya mika mukamin.
A halin da ake ciki, Emeka Beke dan tsagin ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya zama shugaban jam'iyyar bayan ya samu kuri'u 1,570 inda ya kayar da Chizy Nyemosele, in ji jaridar The Nation.
Mathew Adoyi-Omale, sakataren kwamitin majalisar gangamin ta jihar Ribas wanda ya sanar da sakamakon, ya bayyana tsarin zaben a matsayin na gaskiya da adalci.
Sai dai, Chioma, wanda ya fice daga takarar kujerar shugabancin a karshe ya bayyana tsari da sakamakon zaben a matsayin mara inganci.
Ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben.
Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha
A wani labarin, Jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta gudanar da taron gangami na jihohi a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba, inda aka yi zaben shuwagabannin jam'iyyu na jihohi a fadin Najeriya.
Sai dai, jihohi da yawa sun ga sabon lamari tare da fitowar mambobi biyu na zartarwa yayin da jam’iyya mai mulki ke fafutukar ganin ta gyara gidanta kafin 2023.
A kasa mun kawi jerin jahohin da jam'iyyar APC mai mulki ta samar da wakilan zartarwa guda biyu sabanin daya da ya dace.
Asali: Legit.ng