Zaben 2023: Ku daina yi mana barazana, Dattawan Arewa ga Kudancin Najeriya
- Ana cigaba da cacan baki tsakanin Kudu da Arewa kan shugabancin kasa a 2023
- Yayinda dattawan kudu sukace mulki ya dawo hannunsu, na Arewa sun ce ba dole
- Kakakin dattawan Arewa ya ce kawai a mayar da hankali wajen samar da dan Najeriyan da ya cancanta
Kungiyar dattawan Arewa ta gargadi kungiyar dattawan Neja Delta (PANDEF) kan barazanar da take yiwa Arewa kan lamarin wanda zai zama shugaban kasa a 2023.
Kungiyar ta yi raddi ne kan jawabin PANDEF na cewa Arewa ta jira sai 2031 kafin ta sake samun kujeran Shugaban kasa.
A jawabin da Kakakin PANDEF, Ken Robinson, ya saki, ya ce Arewa ta daina tunanin sake samun kujeran Shugaban kasa bayan mulkin Buhari.
Martani kan hakan, Kakakin Dattawan Najeriya, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya gargadi PANDEF da sauran kungiyoyin kudu cewa babu wanda ya isa ya yiwa Arewa barazana.
A hirarsa da DailyTrust ta ruwaito, yace:
"Maganar gaskiya itace duk abinda PANDEF tace, hakkin kowani dan Najeriya ne zaben wanda yake so kuma wajibi ne a girmama hakkin jam'iyyun siyasa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Arewa shirye take da ta zauna da kowa don tattauna yadda za'a yi, amma ba za'a cimma komai ta barazana ba, kuma muna jaddada cewa a daina yiwa Arewa barazana, babu wanda zai iya bamu tsoro."
Baba-Ahmad ya yi kira ga kungiyoyin su mayar da hankali wajen samar da dan Najeriyan da ya cancanta kuma zai hada kan jama'a.
Gwamnonin kudu maso gabas sun yanke hukunci na ƙarshe kan shugabancin 2023
Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki dukkan jam'iyyun siyasar kasar da su zabi 'yan takarar shugaban kasa na 2023 daga shiyyar.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, yayi wannan kiran ne a ranar Juma'a, 8 ga watan Oktoba.
Gwamna Umahi ya lura cewa yankin da Ibo ta mamaye ya sadaukar da abubuwa da yawa kuma dole ne a ba shi damar samar da shugaban kasar na gaba ko ta hanyar shiyya ko ta sabanin haka.
Asali: Legit.ng