Tambuwal: Zamu zauna da Atiku domin duba yuwuwar sulhu wajen tsayar da ɗan takara a 2023
- Gwamnan Sokoto kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP yace zasu zauna da Atiku Abubakar domin yin sulhu game da 2023
- Aminu Waziri Tambuwal ya ce yana da kwarewar da zai kawo wa jam'iyyar PDP nasara, amma ba yana nufin ya fi kowa ba
- Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Tambuwal, Saraki da gwamnan Bauchi sun amince da bin hanyar sulhu
Sokoto - Ɗan takarar shugaban ƙasa kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce zai tattauna da Atiku Abubakar domin duba yuwuwar fitar da ɗan takarar PDP ta hanyar sulhu.
Gwamna Tambuwal ya faɗi haka ne yayin da yake hira a cikin wani shiri na kafar watsa labarai, Channels TV ranar Talata.
Wannan cigaban na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Tambuwal, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, sun amince da fitar da mutum ɗaya a cikinsu.
Da yake tsokaci ranar Talata, gwamnan Sokoton ya ce yana da nagartar da ake bukata wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da yake bayyana Atiku da, "Kawunsa," Tambuwal ya ce, "ina matukar ganin girmansa."
"Aiki ne da muka fara, muna tattauna wa tsakanin mu kuma zamu fuskanci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da sauran yan takara a PDP."
"Zamu yi haka ne domin mu dawo mu haɗa kan mu, muga yadda zamu haɗa kan jam'iyya, mu rage mata ruɗanin siyasa, idan zai yuwu mu duba yuwuwar yin sulhu."
"Ba wai ina cewa na fi kowa bane, a'a ina dai da kwarewa, musamman a irin yadda Najeriya ta koma yanzu, zan iya kawo wa jam'iyyar PDP ɗumbin ƙuri'u."
A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta gamu da babbar matsala, wani jigo tare da dandazon masoya sun koma PDP
Jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da wani cikas a Kwara yayin da take shirin babban gangamin taro na ƙasa ranar Asabar.
Tsohon ɗan takarar gwamna kuma jigo a APC ya jagoranci dandazon masoya sun koma jam'iyyar PDP mai hamayya.
Asali: Legit.ng