Da Duminsa: Bola Tinubu ya gana da Gwamnan APC da Kotu ta tsige a Abuja
- Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamna Umahi na jihar Ebonyi a Abuja ranar Jumu'a
- Gwamna Umahi da kuma Tinubu na cikin kusoshin APC da suka bayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023
- Har yanzun babu wasu bayanai game da abun da manyan yan siyasan biyu suka tattauna a taron na su
Abuja - Jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, sun gana da juna a babban birnin tarayya Abuja, ranar Jumu'a.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da hadimi na musamman na gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwaze, ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook.
Hadimin gwamnan ya kuma sanya Hotunan manyan jiga-jigan siyasar biyu, amma bai bayyana abubuwan da suka tattauna ba.
A rubutunsa hadimin gwamnan ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ɗan takarar shugaban ƙasa, kuma gwamnan jihar Ebonyi, Injiniya David Umahi, ya gana da Alhaji Bola Ahmed Tinubu, a birnin tarayya Abuja, ranar Jumu'a 11 ga watan Maris, 2022."
Wannan na zuwa ne yayin da babban taron jam'iyyar APC na ƙasa ke kara matsawo, wanda aka tsara gudanarwa ranar 26 ga watan Maris, 2022.
Me suka tattauna a wurin ganawar?
Har yanzun babu wani bayani da ya fito daga bangarorin kusoshin jam'iyyar APC guda biyu game da abin da suka maida hankali a wurin ganawar.
Gwamna Umahi na jihar Ebonyi, ya bayyana sha'awarsa ta neman takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, domin ɗorawa daga inda Buhari zai tsaya.
Sai dai a halin yanzun, gwamnan na tsaka mai wuya biyo bayan hukuncin babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, wacce ta yanke kwace kujurarsa ta gwamna da ta mataimakinsa.
Kotun tace tun da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, kuma mutane sun zabe shi a jam'iyyar PDP, kuri'un na jam'iyya ne ba na ɗan takara ba a cewar alkalin.
A wani labarin kuma Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari a 2023
Wani mutumi ɗan asalin jihar Kano ya kuduri aniyar yin tattaki tun daga Abuja zuwa Legas domin nuna wa Tinubu ana tare.
Hussein Lawan ya ce zai yi wannan sadaukarwa ne a madadin matasa ya roki Tinubu ya fito takara don tallafawa matasa.
Asali: Legit.ng