Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe kujerun Ciyamomi 17 da Kansiloli 260 a Enugu

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe kujerun Ciyamomi 17 da Kansiloli 260 a Enugu

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Enugu (ENSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar da aka kammala
  • Shugaban hukumar yace jam'iyyar PDP ta lallasa abokan hamayyarta, ta lashe kujerun ciyamomi da na Kansiloli baki ɗaya
  • A cewarsa, zaben ya gudana cikin nasara da kwanciyar hankali, kuma an yi shi sahihi ba bu cuta babu cutarwa

Enugu - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Enugu, ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi da aka kammala a fadin rumfunan zaɓen jihar.

TVC News ta rahoto cewa hukumar zaɓen ENSIEC, ta bayyana yan takarar jam'iyyar PDP a matsayin waɗan da suka samu nasara a baki ɗaya kujerun kananan hukumomi 17 da Kansiloli 260.

Taswirar jihar Enugu
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe kujerun Ciyamomi 17 da Kansiloli 260 a Enugu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake bayyana sakamakon a hedkwatar hukumar ENSIEC, shugaban hukumar zaben, Dakta Mike Ajogwu, yace an gunar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da sahihanci.

Kara karanta wannan

Daruruwan mambobi a mahaifar dan takarar gwamna na PDP sun sauya sheka zuwa APC

Kazalika ya ce an gudanar da zabem bisa turban kundin dokokin zaɓe, kuma ya yi dai-dai matakai da jadawalin da hukumar ta tsara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakamakon zaɓen Kansiloli

Dakta Ajogwu ya ƙara da cewa baturen zaben kowace gunduma a faɗin jihar ya sanar da sakamakon zaɓen kowane kansila a gundumar da aka zaɓe shi.

Premium times ta rahoto Ya ce:

"Yan takarar jam'iyyar PDP ne suka samu nasarar a zaɓen a gundumomi 260 kuma an bayyana su a matsayin zababbu."

PDP ta lashe Ciyamomi 17

Shugaban hukumar ENSIEC, wanda shi ya bayyana sakamakon zaɓen Ciyamomi, ya ce yan takarar jam'iyyar PDP ne suka samu rinjayen kuri'u a baki ɗaya kananan hukumomin 17 na jihar Enugu.

Ya karisa da bayyana yan takarar PDP a matsayin waɗan suka zama zaɓaɓɓun Ciyamomi.

A wani labarin kuma mun tattara Muhimman abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da mataimakin gwamna Mahdi Aliyu da Majalisa ta tsige a Zamfara

Kara karanta wannan

Da dumi: Mutum 2 sun hallaka, an yiwa wasu jina-jina a zaben deleget na PDP

A ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, 2022, majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamna, Barista Mahdi Aliyu Gusau.

Tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga PDP zuwa APC, alaƙa tai tsami tsakanin su, mun tattaro muku abu hudu game da Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262