Wata Sabuwa: Kawunan gwamnonin PDP sun rabu kan tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023

Wata Sabuwa: Kawunan gwamnonin PDP sun rabu kan tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Gwamnonin PDP sun samu rabuwar kai a tsakanin su kan yankin da zasu kai tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023
  • Gwamnonin Kudu da suka fi yawa sun matsa kaimi kan dole sai yankinsu, yayin da na Arewa suka ce ba zata saɓu ba
  • Shugaban PDP na ƙasa ya jaddada cewa har yanzun jam'iyya ba ta kai ƙarshe kan lamarin yankin da zai fitar da ɗan takara ba

Sabani ya tsananta tsakanin mambobin kungiyar gwamnonin PDP kan yankin da ya kamata jam'iyya ta kai tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023.

The Nation ta rahoto cewa gwamnonin 8 da suka fito daga kudancin Najeriya sun matsa kaimi kan matsayarsu wajibi mulki ya koma yankin su.

Haka nan kuma, huɗu daga cikin gwamnonin arewa 5 sun yi hannun riga da yan uwansu na kudu, inda suka jaddada cewa har yanzun arewa ya dace ta rike tikiti.

Kara karanta wannan

Ku mika wuya tun kafin mu iso maɓoyarku, Sabon Kwamishina ya aike da sako ga yan bindiga

Sannan sun amince a buɗe dama ga kowane ɗan takara ya nemi tikiti saboda za su iya amfani da damar yawan adadin wakilai dake jihohi 19 a arewa.

Gwamnonin PDP
Wata Sabuwa: Kawunan gwamnonin PDP sun rabu kan tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Majiya a cikin jam'iyyar PDP ta shaida wa wakilin mu cewa gwamnonin kudu sun matsa kan matakin da kungiyarsu ta gwamnonin Kudu ta ɗauka cewa wajibi mulkin Najeriya ya koma hannun ɗan kudu a 2023.

Wace matsala wannan rikicin ya haifar?

Wata majiya kusa da kungiyar gwamnonin PDP ta shaida cewa lamarin ya ɗau zafi, ya fara raba kan gwamnonin, kowa ya rike matsayarsa da ƙarfi.

Majiyar da ya nemi a sakaya bayanansa saboda ba'a ba shi damar tsokaci kan lamarin ba, ya ce gwamnonin Kudu sun jaddada cewa ba zasu canza abin da suka amince da shi na mulkin karba-karba ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abba Kyari ya yi magana, ya bayyana kungiyoyi biyu dake kokarin ganin bayansa

"Lamarin ya yi girma sosai ga gwamnonin Kudu duba da cewa Shugaba Buhari, wanda ɗan arewa ne, zai shafe wa'adin mulki biyu shekara 8 a 2023."
"Yanzu ta ya gwamnonin za su koma su shaida wa mutanen su cewa sun sake amincewa a kai tikitin takarar shugaban ƙasa Arewa?"
"Saboda haka suna ganin idan suka yi haka sun yi watsi da matsayar da mambobin kungiyarsu 17 suka amince da shi. wannan matakin ne a kan su."

Kungiyar gwamnonin kudu karkashin jagorancin Rotimi Akeredolu, na jihar Ondo, a wani taro da suka gudanar a baya, sun yanke cewa matukar ana son yin gaskiya, adalci da dai-daito, wajibi mulki ya koma kudu.

Suwa ke neman tikiti a cikin gwamnonin?

An samu rabuwar kai tsakanin gwamnonin arewa kasancewar biyu daga cikinsu na sha'awar tikitin takarar shugaban ƙasa karkashin PDP.

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed., da na Sokoto, Aminu Tambuwal, su ke neman samun tikitin takara, amma suna da babban kalubale na fuskantar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Zamfara: Majalisa ta sake aike wa da zazzafan sako ga mataimakin Matawalle kan batun tsige shi

Kazalika, akwai sabani tsakanin gwamnonin Kudu kan tikitin, domin ana tsammanin mutum uku daga cikinsu na sha'awar zarcewa kujera lamba ɗaya.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa sun boye manufarsu ne har sai lokacin da jam'iyya ta ɗau matsaya kan yankin da zata baiwa Tikiti.

Dakta Iyorchia Ayu, dake jagorantar kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa, na cigaba da jaddada cewa har yanzun ba su cimma matsaya kan tikiti ba.

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan APC da Mambobi sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa PDP a jiha daya

Yayin da jam'iyyun siyasa ke shirin zaben 2023 dake tafe, Jam'iyyar PDP ta yi manyan kamu a jihar Bayelsa ranar Talata.

Wasu jiga-jigan APC da kuma dubbannin mambobin jam'iyyar sun sauya sheka zuwa PDP a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262