Gwamnan Arewa ya tarbi dandazon mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jiharsa

Gwamnan Arewa ya tarbi dandazon mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jiharsa

  • Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya karbi sabbin mambobin PDP da suka sauya sheka daga APC a fadar gwamnatinsa
  • Dandazon mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP a yankin Awalah dake cikin kwaryar birnin Bauchi ranar Lahadi
  • Hadimin gwamna kan harkokin matasa, Alhaji Chiroma, shi ne ya jagoranci masu sauya shekar zuwa wurin mai girma gwamna

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya karɓi dandazon mambobin jam'iyyar APC daga yankin Awalah dake cikin kwaryar birnin Bauchi, waɗan da suka sauya sheka zuwa PDP.

Jaridar This Day ta rahoto cewa bayan sauya sheƙarsu zuwa PDP ranar Lahadi, hadimin gwamna kan harkokin matasa, Alhaji Bala Saleh Chiroma, ya jagorance su zuwa wurin gwamna.

Chiroma ya kai tsofaffin mambobin APC wurin gwamnan ne domin ya karɓi tubarsu a hukumance a matsayinsa na jagoran PDP a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Rudani: An sauke babban sarki a Bayelsa jim kadan bayan an ceto kwamishina daga hannun 'yan bindiga

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed
Gwamnan Arewa ya tarbi dandazon mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jiharsa Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Mutanen da suka sauya sheƙan sun mallaka ofishin APC da suke amfani da shi ga gwamna Muhammed domin a maida shi hannun sabuwar jam'iyyar su PDP.

Da yake kaddamar da ofishin, Muhammed, yace mutanen da suka sauya sheƙan sun ɗauki matakin da ya dace na ficewa daga APC zuwa PDP.

Ku jawo mana sauran yan APC - Gwamna

Ya kuma tabbatar musu cewa gwamnatinsa ba zata nuna banbanci ba domin su ma mambobin PDP ne a yanzu, ya roki su gaggauta rijista domin karɓan katin zama mamba a PDP.

Kazalika gwamnan ya roke su da su jawo hankalin sauran 'ya'yan APC domin su dawo cikin PDP mai mulkin jihar Bauchi.

Muhammed ya ce:

"Bayan ilimanar da mambobin APC ku yi kokarin tattara mana su, ku jawo mana ra'ayin su zuwa jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Jam'iyyar PDP ta dakatar da Surukin gwamnanta da wasu jiga-jigai uku, zasu koma APC

Meyasa suka koma PDP?

Mai magana da yawun waɗan da suka sauya sheƙan, ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ƙauracewa APC ne saboda nasarorin da gwamnatin Bauchi ta samu.

A cewarsa, cigaban da gwamnatin PDP ta kawo jihar cikin shekara biyu da zuwanta ya zarce wanda APC ta yi a tsawon shekara hudu da ta shafe.

A wani labarin na daban kuma Mambobin APC sama da 11,000 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP

Yayin da babban zaɓen 2023 ke kara ƙaratowa, dubbannin mambobin APC sun fice daga cikin jam'iyyar, sum koma PDP.

Lamarin baiwa APC daɗi ba, inda kakakin APC reshen jihar Gombe, ya maida zazzafan maratani ga waɗan da suka sauya shekan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262