Bayan sanar da shugaba Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zaiyi gogayya da Tinubu a 2023
- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, yace kusancinsa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yasa yake son dora wa daga inda ya tsaya
- Gwamnan yace dumbin ayyukan da ya yi wa mutanen jiharsa kaɗai sun isa ya nemi takara a 2023 domin kwatanta haka a ƙasa
- A cewarsa, matsalar yan kungiyar IPOB da shugabansu zata zo karshe matukar ya zama shugaban kasa
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bayyana babban dalilinsa tare da ƙarin haske kan takarar shugaban ƙasar da zaiyi a 2023.
Umahi, wanda ya bayyana kudirinsa na takara a 2023 ranar Talata, yace yana da yaƙinin nasarar da ya samu a jiharsa, ita ake bukata a matakin kasa.
Gwamnan ya faɗi haka ne yayin fira da kafar watsa labarai ta Channels Tv, a cikin shirin 'Siyasa a yau'.
Yayin da aka tambaye shi meyasa yake son ya gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Umahi yace:
"Ina ji a jikina cewa ƙasar nan ta hau kan wani siraɗi, kuma ina da karfin yaƙinin taimakon da Allah ya mana a Ebonyi, har muka samu nasarori ta kowane ɓangare, idan muka samu dama, zamu iya kwatanta hakan a matakin ƙasa."
Kusanci na da Buhari ta sa na fahimci manufofinsa - Umahi
Bayan haka, ya bayyana cewa kyakkyawan kusancin dake tsakaninsa da Buhari, ya sa ya fahimci manufofin shugaban ƙasa a kan Najeriya kuma ya nuna sha'awar ɗorawa daga inda Buhari ya tsaya.
"Wannan shi ne fatan da nake kullum, cewa mu ɗora daga inda Buhari zai tsaya. Ina daga cikin na kusa da Buhari, na san manufarsa ga ƙasa da burinsa."
"Ina tunanin na fahimci shirinsa da kudurorinsa da gaskiyarsa, zamu ƙara da wasu da muka aiwatar a Ebonyi, domin taimaka wa ƙasa baki ɗaya."
Yadda zamu magance matsalar tsaro - Umahi
Gwamna Umahi, ya ƙara da cewa zai bi hanyar maslaha ta siyasa domin kawo ƙarshen kalubalen tsaron da ya addabi kudu maso gabas.
A cewarsa, matukar shugaban kungiyar yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, dake tsare a hannun jami'an tsaro, zai yarda a tattauna, zaman lafiya zai dawo yankin baki ɗaya.
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta bayyana mutanen da take zargin suna da hannu a ta'addancin yan bindiga
PDP ta yi kira da babban murya ga hukumomin tsaro su kira shugabannin APC mai mulki domin amsa tambayoyi kan alaƙa da yan ta'adda.
PDP tace bai kamata jami'an tsaro su kyale ikirarin da tsohon jigon APC ya yi ba kan shigo da yan ta'adda Najeriya a 2015.
Asali: Legit.ng