‘Sai Naga Karshen Shekarar 2025’: Jarumar Fim Ta Mutu Awa 24 da Yin Bidiyo

‘Sai Naga Karshen Shekarar 2025’: Jarumar Fim Ta Mutu Awa 24 da Yin Bidiyo

  • Fitacciyar jarumar fina-finai a Najeriya ta yi wani irin mutuwa na al'ajabi bayan sake bidiyo awa 24 da suka gabata
  • Jarumar kuma mai shirya fina-finai, Allwell Ademola, ta rasu tana da shekaru 43 sakamakon bugun zuciya
  • Abokan aikinta a masana’antar sun bayyana alhini da jimami suna bayyana mutuwarta a matsayin babban rashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos – An tabbatar da rasuwar fitacciyar jarumar Nollywood kuma mai shirya fina-finai, Allwell Ademola.

Jarumar ta rasu tana da shekaru 43 awa 24 bayan ta sake bidiyo cewa sai taga karshen shekarar 2025.

Yar fim ta mutu awa 24 bayan sakin bidiyo
Fitacciyar jarumar fim, Allwell Ademola. Hoto: allwellademolaa.
Source: Instagram

Yadda jarumar fim ta mutu saboda bugun zuciya

Rahoton Leadership ya bayyana cewa jarumar ta rasu ne a ranar Asabar, 27 ga watan Disambar shekarar 2025 da muke ciki.

Bayanan da suka fito sun nuna cewa Allwell Ademola ta mutu ne bayan da ta kamu da bugun zuciya a gidanta.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, cikakkun bayanai game da mutuwarta na ci gaba da kasancewa cikin sirri tsakanin ‘yan uwanta da abokan aikinta.

Allwell Ademola ta fito daga fitaccen gida, kasancewarta jikar marigayi Sir Adetokunbo Ademola, shahararren lauya kuma tsohon Babban Alkalin Alkalan Najeriya.

An yi rashin yar fim a Najeriya
Jarumar fina-finan Nollywood, Allwell Ademola. Hoto: allwellademolaa.
Source: Instagram

Alhinin jaruman Nollywood game da rashin

Mutuwarta ta janyo girgiza da alhini a Nollywood, inda fitattun jarumai suka bayyana jimaminsu ta kafafen sada zumunta.

Jaruma Faithia Williams ta yi jimamin rashin jarumar inda take cewa:

“Haaaa. Wannan labari ya girgiza ni sosai. Eniobanke. Allahu Akbar… Allwell.”

Haka zalika, shahararriyar jaruma Mide Martins ta wallafa hoton marigayiyar tana cewa:

“Asabar mafi muni … Wannan ba adalci ba ne. Allah ya gafarta miki kura-kuranki, Allwell.”

Wani jarumi, Damola Olatunji, ya wallafa hoton kyandir yana cewa:

“Rayuwa mafarki ce.”

Ita ma jaruma Bidemi Kosoko ta nuna rashin yarda da labarin, tana cewa ba za ta iya amincewa da mutuwar ba, tare da yin addu’ar Allah ya hana faruwar hakan.

Rasuwar Allwell Ademola ta bar babban gibi a masana’antar Nollywood, inda jama’a da dama ke ci gaba da yi mata addu’ar rahama da kuma jajantawa iyalanta da masoyanta.

Kara karanta wannan

Bayan harin Amurka, Akpabio ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro

Wani mai amfani da shafin Facebook Ogundele Olugbenga ya wallafa bidiyon inda take waka za ta karshen shekarar 2025.

Kasa da awanni 24 kafin a sanar da rasuwarta, jarumar mai shekaru 43 ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram, inda aka gan ta tana rera wakar addu’ar neman tsira har zuwa karshen shekara.

“Da sunan Yesu, zan ga karshen wannan shekara; wannan shekara ba za ta ga karshena ba.”

Auren jarumar fim, Anita ya mutu

Mun ba ku labarin cewa yar fim a Nollywood, Anita Joseph, ta bayyana cewa aurenta da Fisayo Michael da aka fi sani da MC Fish Michael ya zo ƙarshe.

Rahotanni sun bayyana cewa jarumar ta ce ta yanke wannan shawara ne bayan dogon lokaci tana tunani da neman samun sauki.

Bayaninta ya kawo karshen jita-jita da suka dade suna yawo game da halin da aurensu ke ciki, musamman a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.