‘Na Fi Gamsuwa da Sarautar Naziru’: Mawaki Ya Tabo Rarara bayan Samun Matsayi
- Malam Yahaya Makaho ya yi magana kan sarautar Sarkin wakar kasar Hausa da aka ba Dauda Kahutu Rarara
- Makaho ya nuna damuwa game da sarautar inda yake cewa Daura ba ta wakiltar daukacin kasar Hausa
- Mawakin ya jaddada cewa babu Sarkin kasar Hausa a yanzu, don haka babu ikon nada sarauta irin haka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarautar da aka ba mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara na ci gaba da tayar da kura musamman a tsakanin mawaka da kansu.
Malam Yahaya Makaho ya bayyana matsayarsa game da sarautar Sarkin wakar kasar Hausa da aka ba Dauda Rarara a garin Daura.

Source: Facebook
Yahaya Makaho ya soki sarautar Dauda Kahutu Rarara
Legit Hausa ta samu hirar Makaho ne daga shafin AGG Multimedia Services da aka wallafa a Facebook a jiya Talata 23 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Dauda Kahutu Rarara zai bude fadar Sarkin Wakar Kasar Hausa a Najeriya
Makaho ya ce bai gamsu da sarautar da aka ba Dauda Kahutu Rarara ba, ya ce Daura daban da kasar Hausa.
Ya ce a yanzu babu Sarkin kasar Hausa kuma tun da haka ne babu Sarkin da zai ba da sarauta a madadin kasar Hausa.
Ya ce:
"Ita sarauta suna ta tara, akwai sarauta akwai dabara, mu a kasar Hausa, ba mu da Sarkin kasar Hausa.
"Babu Sarkin kasar Hausa, idan babu shi ta yaya za a samu Wamban kasar Hausa da Sardaunan kasar Hausa da sauransu?, na so Sarkin Daura kawai ya ba Rarara Sarkin wakar Sarkin Daura."

Source: Facebook
'Sarautar Naziru, Ala sune mafi dacewa' - Makaho
Mawakin ya ce ya fi gamsuwa da sarautar da aka ba Naziru da Alan waka da kuma Adamu Hassan Nagudu da sauransu.
Ya ce Sarkin Daura ba shi ne shugaban majalisar sarakuna a Katsina ba ma, bare kasar Hausa gaba daya duba da cewa bai da ikon kan haka.
" Ni a wurina, sarautar da aka yi wa Naziru da Ala da Adamu Hassan Nagudu ta fi ta Rarara dacewa saboda an yi sarautu ne wadanda tunanin kowa zai dauka.
"A Katsina ma fa, ba Sarkin Daura ba ne shugaban majalisar sarakuna, Sarkin Katsina ne ke da wannan muƙamin, to yaya Sarkin Daura zai ba da sarautar kasar Hausa.
"Ka taba ganin gwamna ya samar da hadimi na kasa, ka taba ganin gwamna ya samar da Kwamishina na kasa? Ba zai yiwu ba.
"Sarkin Daura zai iya ba da sarauta a Daura kadai, duk wata sarautar kasar Hausa daga gare shi hauragiya ce kawai."
- Yahaya Makaho
Naziru ya magantu kan sarautar Rarara
Mun ba ku labarin cewa mawaki Naziru Ahmad ya ce sarautar Sarkin Wakar Ƙasar Hausa suna ne na karramawa, ba sarauta ce da ke sanya wasu mawaka a ƙarƙashinta ba.
Ya jaddada cewa a fahimtar ilimi da tsarin mulki, babu wani mawaki da zai tilasta wa wasu yin rajista ko biyayya gare shi saboda wata sarauta ba.
Naziru ya taya Dauda Kahutu Rarara murna, yana mai cewa karramawar ba za ta janyo rashin jituwa ko hassada a tsakanin mawakan Hausa ba.
Asali: Legit.ng
