Wata Sabuwa: Dauda Kahutu Rarara Zai Bude Fadar Sarkin Wakar Kasar Hausa a Najeriya

Wata Sabuwa: Dauda Kahutu Rarara Zai Bude Fadar Sarkin Wakar Kasar Hausa a Najeriya

  • Dauda Kahuru Rarara ya bayyana shirinsa na bude fadar Sarkin Wakar Kasar Hausa a Najeriya, ya ce zai hada kan mawakan Hausa
  • Fitaccen mawakin ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan Sarkin Daura, Faruq Umar Faruq ya nada shi a matsayin Sarkin Wakar Kasar Hausa
  • Rarara ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan sarauta musamman saboda yadda jama'a suka karbe ta kuma suka taya shi murna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fitaccen mawakin nan, Dauda Adamu Abdullahi, wanda aka fi sani da Dauda Kahutu Rarara ya nuna farin cikinsa kan nadin sarautar da Sarkin Daura ya masa.

Dauda Rarara, wanda ya yi fice a fagen wakar siyasa da ta sarauta, ya bayyana shirinsa na bude fadar Sarkin Wakar Kasar Hausa.

Kara karanta wannan

Rarara ya faɗi yadda ya gawurta a waka maimakon gadon karatun Kur'ani

Dauda Kahutu Rarara.
Shahararren mawakin siyasa kuma Sarkin Wakar Kasar Hausa, Dauda Kahutu Rarara Hoto: Mubarak Dabai
Source: Facebook

Mawakin ya fadi haka ne a wata hira da jaridar BBC Hausa, amma bai bayyana a wane wuri ko jihar da zai bude wannan fada ba, amma ya ce zai yi kokarin hada kan mawaka don inganta sana'arsu.

Rarara zai bude fadar Sarkin Waka

Dauda Kahutu Rarara ya kuma kara da cewa bayan bude fadarsa, zai kuma nada hakimai da sauran wadanda za su taimaka wa Sarki wajen gudanar da harkokin mulki.

Idan ba ku manta ba a makonnin da suka shige Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar Faruq ya nada Rarara a sarautar Sarkin Wakar kasar Hausa

Masarautar Daura ta shirya gagarumin bikin nada Rarara, wanda ya samu halartar manyan mutane ciki har da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.

Dauda Rarara ya yi farin ciki da nadinsa

Da yake bayyana yadda yake ji game da wannan nadi, Rarara ya ce yana matuƙar farin ciki da sarautar, musamman yadda jama’a suka karɓe ta hannu bibbiyu, suka taya shi murna.

Kara karanta wannan

Azumi saura wata 2, Sarkin Musulmi ya ba da sanarwar duba watan Rajab

Fitaccen mawakin siyasar ya ce karɓuwar da mutane suka yi wa naɗin ne ya ƙara masa farin ciki da gamsuwa.

Mawaƙin ya ƙara da cewa sarautar ta sa ya yi zurfin tunani game da rayuwarsa, daga inda ya fito zuwa inda ya kai a yanzu.

Dauda Rarara.
Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Adanu Kahutu Rarara Hoto: Mubarak Dabai
Source: Facebook

Ya bayyana cewa ya taso ne a matsayin almajiri, inda yayansa ya kai shi daga garinsu Kahutu zuwa Jihar Kano domin karatun Alƙur’ani.

“Idan na duba rayuwata daga wancan lokaci zuwa yau, sai in ga cewa Allah Ya kai ni wani matsayi da ba zan ƙara nem q ba,” in ji Rarara.

Game da sana’arsa ta waƙa, Rarara ya ce ya kai matsaya ta kololuwa, domin a cewarsa, babu wata daraja da ta wuce a ce ana yi masa kirari da Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa gaba ɗaya.

Rarara ya bayyana gadon gidansu

A baya, kun ji cewa Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa waka haye ya yi, amma gadon gidansu shi ne karatun Alkur'ani mai girma.

Mawaki Rarara ya bayyana cewa bai gaji waka daga wajen mahaifinsa ba, domin a cewarsa karatun Kur’ani aka fi so ya zama ginshiki a rayuwarsa.

Rarara ya kara da cewa mahaifinsa ya yi tsammanin shi ne zai gaji gidansu, ganin yadda aka yi karatu da mahaddata da marubutan AlKur’ani mai tsarki a gidansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262