Bayan Nadin Sarautar Rarara, Naziru Sarkin Waka Ya Fadi Ma'anar Sarkin Mawaka

Bayan Nadin Sarautar Rarara, Naziru Sarkin Waka Ya Fadi Ma'anar Sarkin Mawaka

  • Naziru Ahmad ya ce sarautar Sarkin Wakar Ƙasar Hausa suna ne na karramawa, ba sarauta ce da ke sanya wasu mawaka a ƙarƙashinta ba
  • Ya jaddada cewa a fahimtar ilimi da tsarin mulki, babu wani mawaki da zai tilasta wa wasu yin rajista ko biyayya gare shi saboda wata sarauta
  • Naziru ya taya Dauda Kahutu Rarara murna, yana mai cewa karramawar ba za ta janyo rashin jituwa ko hassada a tsakanin mawakan Hausa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Fitaccen mawakin Hausa, Naziru Sarkin Waƙa, ya yi karin haske kan muhawarar da ta biyo bayan naɗin Dauda Kahutu Rarara a matsayin Sarkin Wakar Kasar Hausa.

Naziru ya bayyana cewa kalmar “Sarkin Waƙa” suna ne ta karramawa kawai, ba sarauta ce ta gargajiya da ke bai wa wanda aka nada ikon mallakar ko jagorantar sauran mawaka ba.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye a Aso Rock

Naziru Sarkin Waka da Rarara
Naziru Sarkin Waka tare da Dauda Kahutu Rarara. Hoto: Barau I. Jibrin|Sarkin Waka
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Naziru Sarkin Waka ya yi ne a wani bidiyo da RFI Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook bayan tattaunawa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bayani ya zo ne bayan kalaman da Rarara ya yi cewa dukkan mawakan Hausa su dawo ƙarƙashinsa, lamarin da ya haifar da rade-radi da tattaunawa a tsakanin jama'a.

Ma'anar Sarkin Waka da sarkin mawaka

Naziru Sarkin Waƙa ya ce a fahimtarsa, “Sarkin Waƙa” suna ne kawai, ba wata sarauta da ke ɗaura sauran mawaka a ƙarƙashin umarnin wanda aka karrama ba.

Ya bayyana cewa da ace sarautar na maido mawaka karkashin mai ita, to da kowane yanki yana da nasa sarkin da mawaka ke ƙarƙashinsa.

Ya ce kamar yadda ya ke Sarkin Waka a Kano, Alan Waka na da sarautar a Dutse, Adamu Nagudu a Borgu, da kuma Dauda Rarara a Ƙasar Hausa.

A bayanin da ya yi, Naziru Sarkin Waka ya ce idan aka nada mutum 'Sarkin Mawaka' ne zai iya jin cewa sauran mawaka na karkashinsa ba 'Sarkin Waka' ba.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Naziru Sarkin Waka ya taya Rarara murna

Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana cewa ya taya Dauda Kahutu Rarara murna bisa wannan karramawa da aka yi masa.

Ya ce babu wata hassada dangane da sarautar da aka ba Rarara, yana mai kara da cewa Rarara da kansa ya taba zuwa ya taya shi murna a wani lokaci.

Taron nada Rarara Sarkin Wakar Kasar Hausa
Wajen taron nada Rarara Sarkin Wakar Kasar Hausa a Daura. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Facebook

A makon da ya gabata ne aka naɗa Dauda Kahutu Rarara a fadar Sarkin Daura a matsayin Sarkin Wakar Ƙasar Hausa.

An gudanar da bikin ne tare da halartar manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasa, ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin.

Rarara ya gana da shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Dauda Kahutu Rarara a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa fitaccen mawakin ya gana da shugaban kasa ne tare da matarsa, Aisha Humaira.

Dauda Kahutu Rarara na cikin manyan mawaka da ke yi wa shugaban kasa da 'yan APC waka a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng