Gwamna Adeleke zai Cigaba da Cire Kunya Yana Tika Rawa a bainar Jama'a

Gwamna Adeleke zai Cigaba da Cire Kunya Yana Tika Rawa a bainar Jama'a

  • Gwamna Ademola Adeleke ya ce rawar da yake yi ba ta rage masa ƙwarewar jagoranci ko kula da aikinsa yadda ya kamata
  • Ya bayyana cewa ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar Accord ne don kare manufofinsa da kuma neman wa’adi na biyu
  • A daya bangaren, jam'iyyar PDP ta danganta ficewarsa da rikice-rikicen cikin gida da ta gaza magancewa tsawon lokaci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya jaddada cewa rawar da yake yi a bainar jama’a ba ta da wani tasiri a kan tsarin mulkinsa ko yadda yake gudanar da ayyukan jiharsa.

Adeleke, wanda ake yi wa lakabi da “gwamnan rawa”, ya sha fuskantar suka daga abokan hamayya da ke cewa fitowarsa wajen rawa alamar rashin kaifin jagoranci ce.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Gwamna Adeleke yana rawa
Yadda gwamna Adeleke ya yi rawa a wani taro. Hoto: Osun State Government.
Source: Facebook

A bayanin da ya yi a hira da Channels TV, gwamnan ya ce wannan dabi’a tasa ce kawai da ya ke yi domin samun nishadi da godiya ga Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Adeleke ya kare rawar da yake yi

Daily Trust ta rahoto cewa Adeleke ya bayyana cewa yin rawa wani ɓangare ne na halayensa tun da dadewa, kuma bai taɓa katse masa aiki ba.

Ya ce kowane mutum yana da hanyar da ya zaba domin hutawa, shi kuwa tasa hanyar ita ce rawa, don haka ba zai daina ba.

A cewarsa, rawar da yake yi ba ta kawar da hankalinsa daga bin diddikin manufofin gwamnati ko kula da al’amuran jama’ar Osun.

Ya jaddada cewa addu’a da godiya ta hanyar rawa wani abu ne da yake ɗauka a matsayin kashin bayan kwanciyar hankalinsa, wanda a ganinsa ma yana ƙara masa kuzari wajen gudanar da aiki.

Dalilan ficewar Adeleke daga PDP

Kara karanta wannan

Abin da Kiristoci suka fadawa dan majalisar Amurka da ya ziyarce su a Najeriya

Adeleke ya bayyana cewa matakin barin PDP ya samo asali ne daga buƙatar “tsare manufofin ci gaban jama’a” da ya fara aiwatarwa, musamman ganin cewa zaben jihar na 2026 na gabatowa.

Ya ce komawa jam'iyyar Accord zai ba shi cikakken kwarin gwiwa wajen ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi gina makarantun zamani, kula da lafiya, inganta albarkatun gwamnati da kuma shirye-shiryen tallafin jama’a.

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke
Gwamna Ademola Adeleke yana zaune a ofis. Hoto: Osun State Government
Source: Instagram

Gwamnan ya ce babu wani abu da ya fi muhimmanci gare shi fiye da ganin tsare-tsaren da ya gadar wa jihar sun kai matakin da ake so, don haka sauya jam’iyya wani mataki ne mai muhimmanci.

PDP ta yi bayani kan ficewar Adeleke

Jam’iyyar PDP ta bayyana ficewar Adeleke daga cikinta a matsayin sakamakon matsalolin cikin gida da aka bari suka yi girma.

Jami’in yaɗa labaran jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce abubuwan da suka faru “ana iya magance su” tun da wuri, amma rashin kula ya bar matsalar ta karu.

Adeleke zai yi takara a jam'iyyar Accord

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya tabbatar da komawa jam'iyyar Accord bayan fita daga PDP.

Kara karanta wannan

"Ka jefa kanka a matsala": PDP ta zargi Gwamna Fubara da rauni bayan komawa APC

Jima kadan bayan koma wa jam'iyyar, gwamnan ya samu damar tsayawa takara a zaben jihar da za a yi a shekarar 2026.

Yayin ba shi damar tsaya wa takara, jam'iyyar ta ce gwamnan ya cika dukkan sharuda kuma ba shi da abokin hamayya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng