'Yar Najeriya da Ta Shirya Kafa Tarihin Kwanciya da Maza 100 a Awa 24 Ta Canza Shawara

'Yar Najeriya da Ta Shirya Kafa Tarihin Kwanciya da Maza 100 a Awa 24 Ta Canza Shawara

  • Fitacciyar mai amfani da kafafen sada zumunta, Mandy Kiss ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan shirinta na kwanciya da maza 100
  • Mandy Kisa ta bayyana cewa wasa take yi domin ba za ta iya daukar maza 100 a kwana guda kacal ba
  • Wannan dai na zuwa nen bayan wani Sarki ya bukaci Gwamnan Legas ya sa a kama Mandy Kiss bisa wannan abu da take shirin yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legas - Shahararriyar mai amfani da kafafen sada zumunta, Ayomiposi Oluwadahunsi, wadda aka fi sani da Mandy Kiss, ta yi amai ta lashe kan shirinta na lalata da maza 100 a awa 24.

Mandy Kisa ta nemi afuwar yan Najeriya, tana mai cewa ta yi haka ne domin jawo hankalin jama'a da kuma yakar talaucin da take fama da shi.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Gwamna ya shiga yanayi, rayuwarsa ta canza bayan rasuwar matarsa

Mandy Kiss.
Hoton fitacciyar mai amfani da kafar sada zumunta, Mandy Kiss Hoto: Real Mandy Kiss
Source: Instagram

Fitacciyar 'yar soshiyal midiyan ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ta saki a shafinta na Telegram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki ya bukaci a kama Mandy Kiss

Hakan dai na zuwa ne bayan Sarkin Iselu a jihar Ogun, Oba Ebenezer Akinyemi, ya nemi Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da ya bada umarnin a kama ta.

Basaraken ya bukaci a kama Mandy Kiss ne saboda yunƙurinta na kafa tarihi da shiga kundin bajinta na Guinness World Records (GWR) ta hanyar kwanciya da maza 100 a cikin awa 24.

Sai dai tuni kundin bajintar ya fito ya yi fatali da shirin Mandy Kiss, yana mai cewa ba a daukar irin wadannan abubuwan da suka shafi saduwa tsakanin mace da namiji.

Mandy ta janye batun lalata da maza 100

A sabon bidiyo da ta wallafa a kafafen sada zumunta, Mandy Kiss ta janye shirin kwanciya da maza 100, tana mai cewa mutane ne ba au fahimce ta amma wasa take yi.

Kara karanta wannan

NiMet: Ruwa da tsawa za su shafi harkokin jama'a a Kano, wasu jihohin Arewa

“Ai wasa nake yi kawai, a kama ni ta yaya? Me ya faru? Nawa ne a asusuna? Ban da kudi da har zan dauki lauya, balle na da bayani ,” in ji ta.

Mandy Kiss ta bayyana cewa ta sanar da shirin kwanciya da maza 100 ne domin ta samu karin daukaka a shafinta da kuma jan hankalin masu bayar da tallace-tallace.

“Ina yi ne kawai don samun nishadi. Na yi hakan ne domin karin daukaka a shafina. Ina bukatar talla. Na yi hakan kawai ne domin neman yadda zan rayu, talauci ya dame ni” in ji ta.
Mandy Kiss.
Hotunan fitacciyar yar soshiyal midiya, Mandy Kiss Hoto: Real Mandy Kiss
Source: Instagram

"Ba zan iya ba" - Mandy ta nemi afuwa

Mandy Kiss ta kuma roki ‘yan Najeriya da kada su dauki maganganunta da gaske, inda ta jaddada cewa ko jiki ba zai iya daukar irin wannan nauyi ba, in ji Tribune Nigeria.

“Ba zan iya yin jima’i da maza 100 ba. Don Allah ku ji tausayina, ‘yan Najeriya, kada ku kai ni gidan yari. Wasa nake yi, ba zan taba iya yin hakan ba, idan na yi haka mutuwa zan yi.

An rufe shafukan miliyoyin 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13,597,057 a dandalin TikTok, Facebook, Instagram da kuma X watau Tuwita.

Wannan mataki ya fito ne daga rahoton bin Dokar CoP ta 2024 da masu gudanar kamfanonin shafukan sada zumunta suka mika wa gwmanatin Najeriya.

Gwamnatin ta kara da cewa an goge wallafe wallafe 58,909,112 daga shafuka daban daban saboda karya doka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262