“Tsoron Yin Aure Nake Yi’: Jarumar Fina Finai Ta Fadi Gaskiya kan Rayuwarta
- Jarumar Nollywood, Kiitan Bukola, ta bayyana yadda rashin kulawar uba ya shafi ra’ayinta game da aure da kuma burinta na kafa gida mai inganci
- Kiitan ta ce tana son aure, amma tana jin tsoron samun yara ba tare da aure ba, sakamakon abin da ya faru a rayuwarta a baya
- Jarumar ta tuna yadda ta yi rayuwa cikin talauci da kuma rashin samun kauna kamar yadda iyaye ke yi wa 'ya'yansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Jarumar Nollywood, Kiitan Bukola ta bayyana irin wahalhalun da ta sha a rayuwa da kuma tasirin yarintarta kan ra’ayinta game da aure.
Jaruma Kiitan ta ce ko kadan ba ta sha'awar yin aure hasalima abin tsorata yake yi saboda yadda ta taso.
Fargabar jaruma Bukola kan aure a rayuwarta
A wata hira da ta yi da Biola Bayo da The Nation ta bibiya, Kiitan ta ce tana son aure sosai, amma tana tsoron shiga cikin aure saboda burinta na kafa gida mai zaman lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa tsoronta ya samo asali ne daga yadda ta tashi ba tare da samun kulawar uba ba, wanda ya bar wani gibi a rayuwarta.
"Ina son aure amma kuma a lokaci guda ina matukar tsoro saboda ban son samun 'ya'ya ba ta hanyar aure ba."
“Rashin kulawar uba ya bar min tasiri mai zurfi,wannan jarabawa ta sa nake son kafa gida mai inganci."
“Wasu daga cikin ’ya’yan mahaifina ban san su ba, sai dai wasu na haduwa da su ta yanar gizo, rashin samun soyayyar iyaye ya dame ni sosai."
- Kiitan Bukola
Jaruma ta koka kan halin rayuwarta
Jarumar ta ce tana tsoron samun yara ba tare da aure ba, tana mai cewa tana burin samun iyali mai cike da kauna da kulawa, cewar Daily Post.
Kiitan ta kuma bayyana yadda ta fara rayuwarta cikin wahala, tana tallan tuwo da miyan efo a garin Sabo da ke jihar Ondo.
Jaruma ta fara hsirin hada aure
Kun ji cewa jarumar Nollywood, Chinonso Ukah ta shirya kaddamar da sabuwar manhajar haɗa ƴan mata da samari soyayyar da za ta kai shiga daga ciki.
A wata sanarwa da manajar kamfanin jarumar ta fitar, ta ce an tsara manhajar daidai da zamani domin haɗa ma'aurata.
Asali: Legit.ng