Gwamnoni da Manyan Najeriya Sun Hallara Jigawa Auren 'Yar Gwamna Umar Namadi
- Rahotanni sun nuna an daura auren ‘yar gwamnan ihar Jigawa, Umar A. Namadi a babban masallacin jihar da ke birnin Dutse
- Manyan mutane a Najeriya ciki har da gwamnoni, tsofaffin gwamnoni, ministoci, sanatoci da sauransu sun halarci bikin
- Bayanai sun nuna cewa limamin masallacin Dutse, Sheikh Abubakar Sani Birnin Kudu ne ya jagoranci addu’o’i bayan kammala auren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa – A yau Juma'a, babban masallacin Juma’a na Dutse ya cika da fitattun mutane daga sassa daban-daban na Najeriya domin halartar auren Dr Salama Umar Namadi.
Bikin ya kasance daya daga cikin manyan taruka da suka ja hankalin jama’a a jihar Jigawa a shekarar 2024.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Garba Muhammad ya wallafa bidiyon kai tsaye a Facebook a kan yadda aka daura auren a babban masallacin Dutse.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Auren, wanda aka gudanar karkashin jagorancin Limamin Kafin Hausa, ya samu halartar shugabanni daga matakai daban-daban na gwamnati da kuma manyan malamai na addini.
Manyan baki da suka halarci daurin auren
Daga cikin manyan mutane da suka halarci bikin auren akwai gwamnoni daga jihohi daban-daban.
Gwamnonin Kano, Abba Kabir Yusuf; Zamfara, Dauda Lawal; Gombe, Inuwa Yahaya; Katsina, Dikko Umaru Radda; da Yobe, Mai Mala Buni, duk sun samu halarta.
Hakazalika, tsofaffin gwamnonin Jigawa, Sule Lamido da Saminu Turaki, da kuma tsohon gwamnan jihar Kebbi Atiku Badugu sun kasance cikin mahalarta bikin.
Ministan tsaro, Badaru Abubakar, Ministan Noma, Abubakar Kyari, da Sanata Sabo Muhammad na Kudu, ‘yan majalisar wakilan jihar Jigawa, shugabannin kananan hukumomi sun kasance a wajen.
Bikin ya samu halartar malaman addini ciki har da shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Kabiru Haruna Gombe.
Addu'o'i a auren 'yar gwamna Namadi
Sheikh Abubakar Sani Birnin Kudu ya jagoranci addu’o’in musamman bayan an kammala daurin auren.
Malamin ya yi addu’a domin neman samun zaman lafiya, samun albarka, da dorewar soyayya tsakanin ma’auratan.
Gwamnan jihar Jigawa da mai martaba sarkin Dutse, Hamim Nuhu Muhammad Sanusi na cikin wadanda suka karbi baki yayin bikin.
An kaddamar da aikin ruwan Dutse
A wani rahoton, kun ji cewa an kaddamar da katafaren aikin ruwan Dutse da zai wadatar da miliyoyin al'umma da ruwa mai tsafta.
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce an fara aikin ne shekaru 24 da suka gabata amma ba a karasa shi ba sai a zamanin Umar Namadi aka kara dauko shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng