‘Zama da Kasa da Mata 3 Zunubi ne’: Jarumin Fina Finai Ya Yi Tone Tone

‘Zama da Kasa da Mata 3 Zunubi ne’: Jarumin Fina Finai Ya Yi Tone Tone

  • Jarumin fina-finan Nollywood da ke Kudancin Najeriya, Stephen Alajemba ya ba maza shawara kan yadda za su yi aure
  • Fitaccen jarumin wanda aka fi sani da Uwaezuoke ya ce auren mata daya ko biyu babban hatsari ne kuma barazana a rayuwa
  • Jarumin ya shawarci maza su auri mata uku ko fiye da haka domin za su yi ta masa abin da ya dace shi kuma yana kawo abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Jarumin fina-finan Nollywood, Stephen Alajemba ya yi magana kan yawan mata da mutum ya kamata ya aura.

Jarumin da aka fi sani da Uwaezuoke ya ce zunubi ne mutum ya zauna da kasa da mata uku a rayuwarsa.

Jarumin fina finai ya ba maza shawara kan auren mata fiye da 1 ko 2
Jarumin fina-finai, Stephen Alajemba ya ce hatsari ne zama da mata 1 ko 2. Hoto: @uwaezuoke_fanpage.
Asali: Instagram

Jarumin fim ya ba maza shawara kan aure

Alajemba ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar PM News ta bibiya inda ya ce auren mata daya ko biyu jefa kai acikin hatsari ne.

Kara karanta wannan

'Akwai yunwa': Tinubu ya magantu daga Brazil, ya ba yan kasa satar amsar shirinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumin ya ce duk wanda ya auri kasa da mata guda uku zai fuskanci matsalar rasa ransa ta hanyar zuba masa guba a abinci.

Ya ce auren mace daya kan ma yafi komai hatsari inda ya ce rayuwr mutum tana fuskntar barazana, cewar Daily Post.

'Yawan matan da ya kama ku aure' - Jarumin fim

"Zunubi ne ka auri mata daya ko biyu amma idan ka auri uku ko hudu ka tsira daga zunubi."
"Idan ka auri mata daya rayuwarka na cikin hatsari haka nan idan ka auri guda biyu za su hada baki su zuba maka guba."
"Amma idan ka auri mata uku ko fiye za ka yi ta samar musu da abinci kana shiga dakunansu, kowace za ta yi abin da ya dace."

- Stephen Alajemba

Jarumin fina-finan Nollywood ya bar duniya

Kun ji cewa an yi rashin ɗaya daga cikin fitattun jaruman da ake ji da su a masana'antar fina-finai ta Yarbawa a Kudu maso Yamma na Najeriya.

Kara karanta wannan

'Muna goyon bayanka': Malamin Musulunci ya magantu da Abba Hikima ya maka Wike a kotu

Fitaccen jarumi wanda ya daɗe a masana'antar, Pa Charles Olumo Sanyaolu wanda aka fi sani da Agbako ya yi bankwana da duniya.

Marigayin wanda ya rasu da sanyin safiyar ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoban 2024 ya bar duniya yana da shekara 101 da haihuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.