"Na Shiga Uku": Wani Dan Najeriya Ya Koka Bayan Gayyatar Wata Budurwa Ta Kwana A Gidansa, Ya Wallafa Bidiyo

"Na Shiga Uku": Wani Dan Najeriya Ya Koka Bayan Gayyatar Wata Budurwa Ta Kwana A Gidansa, Ya Wallafa Bidiyo

  • Wani mutum dan Najeriya ya bayyana rashin jin dadi da ya fuskanta bayan ya gayyaci wata budurwa zuwa gidansa ta kwana
  • Mutumin ya bayyana cewa ya gayyace ta gidansa kuma ya kyalle ta ta kwana sannan ta kama hanya ta tafi da safe
  • Amma, a tsakar dare, matar ta yi barci mai nauyi sannan ta fara munshari hakan ya bata masa rai

Wani mutum dan Najeriya ya bayyana abin da ya faru tsakaninsa da wata yarinya da ya gayyata zuwa gidansa ta kwana.

Ya bayyana cewa sun kwanta tare kuma ya yarda ta yi barci a gidansa sai ta tafi da safe.

Matashi
Matashi ya gayyaci budurwa gidansa. Hoto: @horlu_baby
Asali: TikTok

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma a tsakiyar dare, matashin ya kasa yin barci saboda yarinyar tana munshari mai zurfi yayin da suke kwance.

Kara karanta wannan

Ta ya za ki sauko? Budurwar da ta yiwa katuwar giwa hawan doki ta bar jama'a baki bude

Da ya ke wallafa bidiyon a TikTok, mutumin cikin bacin rai ya roki masu bin sa a dandalin sada zumuntar su tallafa masa.

Abin da masu amfani da dandalin sada zumunta suka ce game da bidiyon

@h.afsattt ta ce:

"Karar tamkar janareta."

@irawo4real ya yi tsokaci:

"Ka wahal da ita sosai ne."

@simbioyedele cewa ya yi:

"Da na fada wa yarinyar an kira ni a wurin aiki kuma babu wanda zai taya ni."

@rozay3031 shi kuma ya ce:

"Irin wannan yan matan idan suka yi barci haka sai gobe kenan. Ba abin da za ka iya yi. Na tun wacce na dakko a IB."

@officialamaka09 ya kara da cewa:

"Wane irin abu ne wannan. Ba ma bidiyon ke bani dariya ba, tsokacin da mutane ke yi ne."

Kalli bidiyon a kasa:

An Hana Amfani Da 'Gajeren Siket' A Matsayin Unifom A Makarantun Wata Jiha A Kudancin Najeriya

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Zaba Tsakanin Kishiyar Gida Da Ta Waje, Bidiyon Ya Dauka Hankali

A wani rahoton, gwamnatin Jihar Anambra ta hana saka yan gajerun siket wato 'mini skirt' a matsayin kayan makaranta a dukkan makarantun jihar, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, kwamishinan Ilimi na Jihar Anambra ce ta sanar hakan a Awka a ranar Lahadi tana mai cewa sanarwar haramcin ya zama dole don makarantu za su dawo hutu a ranar Litinin.

Ta ce dai tuni an sanar da sakatarorin ilimi na makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da kan da dokar haramcin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164