Budurwa ta Tafkawa Matashi Asiri Bayan ya Dirka Mata Ciki Ya Musanta, Ya Koma Tsince-Tsince

Budurwa ta Tafkawa Matashi Asiri Bayan ya Dirka Mata Ciki Ya Musanta, Ya Koma Tsince-Tsince

  • Wata mata 'yar Najeriya ta labarta abun da ya faru da tsohon saurayinta wanda ya dirka mata ciki gami da musanta hakan shekaru da suka shude
  • Matashim daga jihar Akwa Ibom wanda makwabcin goggonta ne shekaru 15 da suka shude, ya dirka mata ciki tana shekarar farko a makaranta
  • Musanta cikin da yayi ne yasa ta zubar tare da tafkawa matashin mugun asiri wanda aka yi amfani da jininta aka yi

Wata mata 'yar Najeriya tazo soshiyal midiya da su bata shawarar yadda zata taimaki tsohon saurayinta wanda ke cikin tsananin rayuwa.

Yayin bada labarinsu tare da sakaya suna a wani guruf a Facebook, matar ta bayyana yadda matashin wanda 'dan asalin Akwa Ibom ne ya dirka mata ciki shekaru 15 da suka shude tare da musanta hakan.

Kara karanta wannan

Mahaifi da Yaronsa Sun Hadu Sun Jibgi Ma’aikata Saboda Uwarsu Ta Rasu a Asibiti

Mahaukaci
Budurwa ta Tafkawa Matashi Asiri Bayan ya Dirka Mata Ciki Ya Musanta, Ya Koma Tsince-Tsince. Hoto daga The Cable, YNaija
Asali: UGC

Taje hutu gidan goggonta inda ta hadu da mutumin, wanda makwabcinta ne. A lokacin tana shekarar farko a jama'a, sun tsuduma kogin soyyaya gami da fara fahimtar juna.

Sai dai yayin da rabo ya shiga tsakaninsu, matar ta bayyana yadda ya musanta dirka mata ciki har yayi barazanar sawa a daure ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin da tsohon saurayintan yayi ya matukar bata mamaki. Daga bisani, wata kawarta ta hada ta da wani mai kemis wanda ya taimaka mata wajen zubda cikin.

Matar ta ce cike da radadi tayi masa miyagun addu'oi, sannan ta manta da komai ta cigaba da rayuwa...

Zata yafe masa bayan watanni idan ya nemi yafiyarta

Matar ta yafe mata bayan wasu watanni da ya nemi gafararta. Sai dai, matar bata ji dadin halin da yake ciki yanzu ba. Duk da tayi aure da 'ya'ya biyu.

Kara karanta wannan

Karamar Yarinya ta Cakare Cikin Shigar Amare, Tace Mahaifinta ne Angonta

Ta ce sun hadu a farkon shekarar 2022, inda taga duk ya susuce, ba mata bare 'ya'ya.

"Ya shaidamin cewa, an fada masa nice tushen matsalarsa, na ce masa ni na dade da yafe masa har zuciyata. Amma ganinshi a wannan yanayin ya sani zubda hawaye."

- Kamar yadda ta rubuta.

Martanin jama'a

Chiagozie Okwuaka ta ce:

"Kiyi masa addu'a. Ki roki Ubangiji ya aurar dashi to ya bashi yalwar dukiya. Shi dake yawan yafiya zai yafe masa. Ubangiji ya yafe miki, don me har yanzu kike rike dashi tsawon wadannan shekarun?"

Kate Onyegwara Okoli ya ce:

"Ba ke bace sanadiyyar tabewarsa. Tsumagiyar zaluncinsa ne ke zibgarsa. Ta yuwa yayi hakan ga wasu mata, amma muma mata ya kamata mu daina yin ciki ba tare da aure ba.
"Idan har se kayi, ta rika tunawa da ana siyar da maganin hana daukar ciki da kwaroron roba."

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

Agulue Valentine ta ce:

"Kina so in koma garesa ne ko ki bashi kyautar daya daga cikin 'ya'yanki, don magance laifin da kike ganin naki ne.
"Ki manta dashi sannan ki rika sanya shi a addu'a. Wasu matan, a koda yaushe ina cewa, ana saurin amsar addu'arsu. Idan ka cutar, ita kuma bata da hakki, alhaki zai farauto ka."

Damola Paul ya ce:

"Babu abun da kika jawo... Mugun halinsa ya jawo masa. Ba ke kadai ya cutar ba a wannan rayuwar. Ko dai wani daban ya masa miyagun addu'oi ko kuma alhaki yayi maganin shi. Kin riga kin yafe masa, ki manta da shi ki cigaba da rayuwa, kada ki bari yasa kiji a ranki ko kina da laifi."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng