Mahaifina ne Ango: Yarinya Tayi Shigar Amare, Tace Babanta Zata Aura a Bidiyo

Mahaifina ne Ango: Yarinya Tayi Shigar Amare, Tace Babanta Zata Aura a Bidiyo

  • Wata yarinya karama ta bar mutane baki baki bude, yayin da ta bayyana kamar amarya tare da cewa tana so ta auri mahaifinta
  • Bidiyon mai cike da ban dariya da Nshimba Tshitende Re ta wallafa na nuna yadda yarinyar ke taku 'dai'dai cikin farar doguwar riga da takalman dai suka yi mata yawa
  • An wallafa bidiyon ne ranar 30 ga watan Nuwamba amma har yanzu yana yawo yayin da mutane sama da 344, 000 suka kalla da tsokacin mutane 981.

Bidiyon mai ban dariya da Nshimba Tshitende Re ta wallafa ya nuna yadda wata 'yar yarinya cikin farar doguwar rigar amare.

Karamar Yarinya
Mahaifina ne Ango: Yarinya Tayi Shigar Amare, Tace Babanta Zata Aura a Bidiyo. Hoto daga @TikTok/reninshimba
Asali: UGC

Mahaifin yarinyar ya shiga rudanin ganin yadda 'diyarsa tayi shiga kamar amarya tare yi masa tayin ya aureta.

Bidiyon, wanda ya dauki tsawon minti daya da aka wallafa ranar 30 ga watan Nuwamba ke nuna yadda 'yar yarinyar daga dakinta ta shirya tsaf don aure.

Kara karanta wannan

"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali

Matsalar guda daya ita ce yadda 'yar yarinyar ta bukaci a daura aurenta da babanta, wanda ba abu bane mai yuwuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tana sanye ne da takalmin da yayi matukar mata yawa, wanda hakan ya jawo hankalin masu amfani da kafar TikTok da suka ci karo da bidiyon.

Yayin da mahaifinta ke kokarin fahimtar bukatarta, yarinyar cewa tayi ya kamata a fara shagalin bikin ba tare da wani jinkiri ba.

A kalla mutane 981 sunyi tsokaci karkashin bidiyon, inda a halin yanzu ya samu sama da jinjina 28,000.

Kalla bidiyon a kasa:

Martanin jama'a

@viewsby_nc ta ce:

"Da gaske ta ce "eh mijina?" Kyakyawan mutumi."

@Karabo.nn yayi tsokaci:

"Cewa da tayi "to bari a fara yanzu" daga karshe nawa ne."

@Zimikhitha Cleo Ntuli ya ce:

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

"Yanzu za'a daura mana aure."
“Harma tasan zaka dauki tsawon lokaci kafin amsa mata tambayar."

@Mantsundu tayi tsokaci:

"Duk yara mata suna fadawa soyyayar iyayensu maza. Nima naso auren mahaifina."

Karamar yarinya da ta tashi tare da kaji

A wani labari na daban, wata karamar yarinya ta bayyana a bidiyo cikin shakuwa da kaji har suna wasa.

A bidiyon, an ga yadda kajin ke bin ta kamar bindi sannan take zama cikinsu suna wasanni cike da birgewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel