Bidiyo: Jarumin Fina-Finan Najeriya Ya Ci Karo Da Ƙaton Baƙin Maciji A Ɗakinsa Da Tsakar Dare, Ya Zargi Makiya

Bidiyo: Jarumin Fina-Finan Najeriya Ya Ci Karo Da Ƙaton Baƙin Maciji A Ɗakinsa Da Tsakar Dare, Ya Zargi Makiya

  • Jarumin fina-finan kudancin Najeriya, Kelvin Chizzy ya nuna bacin ransa a soshiyal midiya a yayin da wa wallafa bidiyon bakin maciji da ya ziyarci gidansa cikin dare
  • An jiyo furodusan fina-finan a bidiyon yana tambayar macijin wanene ta turo shi gidansa ya kai masa hari da iyalansa
  • An kuma ji Chizzy yana tsine wa makiyansa da wadanda suka tura masa bakin macijin ya cutar da shi

Jarumin Nollywood kuma furodusa Kelvin Chizzy ya dauki hankulan mutane a intanet da bidiyon da ya wallafa a shafinsa yana mai cewa makiyansa sun turo masa bakin maciji ya kawo masa hari.

Jarumin a bidiyon da ya wallafa a shafinsa ya nuna bakin macijin yana kwance a kasa a wani daki a gidansa.

Chizzy
Jarumin Najeriya Ya Koka A Bidiyo Bayan Wani Bakin Maciji Ya Shiga Dakinsa Da Tsakar Dare. @holylambflims.
Asali: Instagram

An jiyo Chizzy a bidiyon, yana tsinuwa kan macijin yayin da ya ke cewa wadanda suka turo macijin sunyi kuskure domin ubangijinsa baya barci.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Furodusan na fina-finan ya kuma bayyana cewa zai halaka macijin sannan ya kona shi kamar yadda ya nuna a wani bidiyon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga bidiyon bakin macijin da ya ziyarci gidan Kelvin Chizzy a kasa:

Wasu daga cikin martanin da masu amfani da intanet suka yi game da bidiyon Chizzy game da macijin:

@toksduttie:

"Sun rasa mamba daya."

@amandaneoofficial:

"Ba komai bane asiri daga kauye. Damina ne yanzu kuma macijin ya so neman wurin da zai fake ne ko wani abu a gidan ka ya sa ya shigo."

@xiollajohn:

"Kana da juriya fa! Idan da ni ne da a babban hanyar benin za a kama ni."

@seeker_ib:

"Ka tsaftace muhallinka ka dena dora wa abin hallitu laifi."

@stellaidika:

"Ba a sanar da su ba. Daya ya tafi. Allah ya tsare ka."

Kara karanta wannan

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

@white_beauty_paradise:

"Allah ya tona asirinsu."

Sautin Murya: Wata Da Aka Ce Matar Jarumin Fina-Finan Najeriya Ne Ta Masa Fallasa Game Da Yayansa

Labaru marasa dadi ne aka rika dangatawa da Jarumin Nollywood Yekini Higher wanda ake kira Itele.

Jarumin wanda ya sha suka a dandalin sada zumunta a kwanakin baya saboda cin amanar matarsa da wata jaruma, Debankee, ya hadu da fushin matarsa ta biyu saboda rashin kula da yaransu.

Matar, wacce aka ce itace matarsa ta biyu ta tuntubi shafin Gistlover inda ta yi wa jarumin fallasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel