Dattijo Ɗan Shekara 74 Ya Yi Auren Farko A Wata Jihar Arewa, Ya Bayyana Dalilin Rashin Yin Aurensa Da Wuri

Dattijo Ɗan Shekara 74 Ya Yi Auren Farko A Wata Jihar Arewa, Ya Bayyana Dalilin Rashin Yin Aurensa Da Wuri

  • Mallam Muhammad Awal, wani dattijo dan shekara 74 ya yi aurensa na farko a duniya a ranar Asabar 28 ga watan Agustan 2022
  • Awal ya bayyana cewa rashin kudi ne ya hana shi yin aure da wuri domin tuna yana kuriciya ya nemi wasu matan da aure amma ba su daukansa da muhimmanci
  • Dattijon ya angwance ne da matarsa mai suna Mallama Rahmat Muhammad, wata bazawara yar shekara 45 wacce ta ce auren na su ikon Allah ne

Kogi - Wani mutum mai shekara 74 daga Jihar Kogi mai suna Mallam Muhammad Awal, ya yi auren farko a rayuwarsa, rahoton LIB.

Awal ya aure wata bazawara mai shekara 45, Mallama Rahmat Muhammad, a Lokoja, babban birnin jihar Kogi a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Kaduna: Alkalin Kotun Shari'a Zai Biya Wa Salele N100,000 Sadaki Don Auren Sahibarsa Bilkisu

Ango Dan Shekara 74
Hotunan Dattijo Dan Shekara 74 Da Ya Yi Auren Farko A Wata Jihar Arewa Sun Ƙayatar. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rashin kudi ya hana ni aure - Muhammad Awal

Da ya ke magana da manema labarai kan dalilin da yasa ya jinkirta yin aure, dattijon ya ce rashin kudi ne yasa bai nemi wata mace da aure ba.

Ya ce:

"Ina tsoron ba zan iya kula da matata ba idan na yi aure kuma abu ne da na ke tsoro kuma bana wasa da shi. Ina kuma tsoron rabuwa da matata. Na san idan na kasa kula da ita, za ta iya rabuwa da ni ko ta ci amana ta da wani namijin, kuma ba zan so hakan ba, shi yasa na jingine batun aure. Amma, yanzu Allah ya sa na yi."

Ango dan shekara 74
Hotunan Dattijo Dan Shekara 74 Da Ya Yi Auren Farko A Wata Jihar Arewa Sun Ƙayatar. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Matar Awal
Hotunan Dattijo Dan Shekara 74 Da Ya Yi Auren Farko A Wata Jihar Arewa Sun Ƙayatar. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

An masa tambaya shin ko ya taba neman wasu matan a baya da aure, ya kada baki ya ce:

Kara karanta wannan

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

"Na taba ... sau da yawa ma. Lokacin ina da kuriciya. Mafi yawancin su basu dauke ni da muhimmanci ba saboda ba ni da kudi. Amma na gode Allah cewa yanzu abin ya zama tarihi."

Abin da ya bani sha'awa game da matata - Awal

Angon ya ce:

"Baya ga kyawunta, tana da halaye masu kyau da addini kuma ta san menene aure. Allah ne kadai ya san ko za mu haifi 'ya'ya. Babu wanda ya san abin da Allah zai yi. Ba hannun mu abin ya ke ba."

A bangarenta, Rahmat ta ce Allah ya kaddara za su yi aure.

Ta kara da cewa:

"Allah shi ya san dalilin da ya sa ya hada mu kuma addu'a na shine Allah ya mana albarka ya bamu zaman lafiya da fahimtar juna a gidan mu."

Soyayyar Facebook: Mata ƴar Indiya ta fasa auren masoyinta ɗan Najeriya a gaban mutane ranar ɗaurin aure

Kara karanta wannan

“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo

A wani rahoton, wani mutum dan Najeriya ya shiga cikin damuwa bayan matar da zai aura ta yi watsi da shi a yayin da ake daf da daura musu aure, LIB ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a binrin Bangladesh kuma an gano cewa matan da mijin sun hadu ne a shafin dandalin sada zumunta na Facebook.

Daga bisani ne matar ta gayyaci saurayin dan Najeriya zuwa kasarta wato Indiya domin a daura musu aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164