Fusata Na Ke Yi Duk Lokacin Da Aka Kira Ni Kyakyawa, In Ji Shahararren Jarumin Najeriya

Fusata Na Ke Yi Duk Lokacin Da Aka Kira Ni Kyakyawa, In Ji Shahararren Jarumin Najeriya

  • Gogaggen jarumin Nollywood, Charles Awurum, a wani bidiyo da ya wallafa a soshiyal midiya ya ce haushi ya ke ji idan an kira shi kyakyawa
  • Awurum, ya bayyana cewa ya fi son a kira shi mummuna a madadin kyakyawa don hakan yana ganin gaisuwa ne a wurinsa
  • Jarumin barkwancin cikin wani bidiyon ban dariya da ya wallafa ya ce rayuwa fa gwagwarmaya ne, hakan ne dalilin da yasa ake ganinsa yadda ya ke a yanzu

Jarumin fina-finan Najeriya da barkwanci, Charles Awurum, ya ce kwakwata baya fushi idan wani ya kira shi mummuna domin ba shi da kyau.

A wani bidiyo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Instagram, fitaccen jarumin ya ce idan an kira shi kyakyawa, ya kan kule da fushi kuma yana daukan hakan a matsayin zagi don ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Charles Awurum.
Na Kan Ƙule Da Fushi Duk Lokacin Da Aka Kira Ni Kyakyawa, In Ji Shahararren Jarumin Najeriya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ku kalle ni da kyau sosai, Idan mutum ya gan ni kuma yana son zagi na, ya fada min mai gida kai mummuna ne, don Allah ku fada min, wannan zagi ne, ai lokacin da kace min dan uwa kana da kyau sosai, a lokacin ne zan fusata, idan ka ce min ni mummuna ne, wannan gaisuwa ce mai kyau, na gode sosai ... wannan duniyar akwai wahalar rayuwa," a cewar jarumin cikin gajeren bidiyon da ya wallafa.

Awurum na daya daga cikin fitattun jaruman fina-finan kudancin Najeriya wato Nollywood, ya shafe kimanin shekaru 20 a masana'antar.

Ya yi aiki tare da fitattun jarumai irin su John Okafor (Mr Ibu), Nkem Owo (Osuofia), Francin Odega da wasu da dama.

Wasu daga cikin fina-finan da ya yi sun hada da 'Away Match (2007)', 'Fools on the Run (2007)', 'Yahooze Prophets (2009)', 'Most Wanted Kidnappers (2010)', da 'Jack and Jill (2011)' da sauransu.

Kara karanta wannan

Namijin Kirki Ba Zai Yi Soyayya Da Budurwa Fiye Da Shekara Ba Tare Da Ya Aure Ta Ba – Hadimin Gwamna

Martanin wasu yan Najeriya a soshiyal midiya

@charlesinojie:

"Idan dai ba mutum bai da hankali bane. Ya san kai ciyaman ne na munanan. Ko dai mutumin bai da ido ne?

@alibabagcfr:

"Kyakyawan yaroooooooo!.."

@eminent_shipping:

"Duk wanda ya kira ka mummuna a matsayin zagi bai san komai ba. Kai da ke da kyau tamkar aljanin ruwa."

@teeh_lyfstyle:

"Dama ko ba a fim ba haka ya ke magana."

@etimajonathan:

"Ka yi rayuwarka ta gaskiya! Idan ka ce kai mummuna ne, wane ni in ce ba haka ba?".

2023: Zabe Ya Fi Zuwa Coci Da Masallaci, In Ji Jarumin Najeriya Kanayo. O. Kanayo

A wani rahoton, fittacen jarumin Nollywood, Anayo Modestus, wanda aka fi sani da Kanayo. O. Kanayo, ya ce a ra'ayinsa samun katin zabe na PVC ya fi zuwa coci da masallaci.

Jarumin ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Instagram inda ya wallafa bidiyo yana bayani cewa kowanne dan Najeriya na da ikon ceto kasar. Jarumin ya ce duk wani kasa da bai samu katin PVC ba yana cikin matsalar kasa.

Kara karanta wannan

Ka bar ni na more: Uba ya damu da yadda dansa yake hana shi jin dadin aure

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164