Dama ta samu: Yadda kamfani zai biya ku N13.5m kawai don ku kwanta a kan gado

Dama ta samu: Yadda kamfani zai biya ku N13.5m kawai don ku kwanta a kan gado

  • Shin ka taba tsammanin kwanciya zai zama sana'a? To ga dama ta samu ga masu sha'awa
  • Wani kamfani zai ke biyan mutane saboda su kwanta su more a kan katifun da yake kerawa
  • Kamfanin ya bayyana irin miliyoyin da zai biya duk wadanda suke da sha'awar wannan aiki

Baya ga rage damuwa da taimakawa jiki, kwanciya akan gado yana rage gajiya amma a yanzu ya zama damar aiki mai tsoka kamar yadda wani kamfani ke son biyan mutane kudi su kwanta.

Ladbible ta ba da rahoton cewa wani kamfani mai kera gadon alatu da kawa da aka fi sani da Crafted Beds yana karbar cike-ciken mutane don gwajin wata katifa.

Daya cikin gadajen da kamfanin ke kerawa | Hoto: @craftedbeds
Dama ta samu: Yadda kamfani zai biya ku N13.5m kawai don ku kwanta a kan gado
Asali: UGC

Aikin zai ba masu sha'awa £24,000 (N13,589,203.20) a kowace shekara wanda idan aka kasafta shine £2,000 (N1,132,433.60) kowane wata.

Kara karanta wannan

Likitoci sun samu nasarar dasawa dan Adam kodar Alade a Amurka

Za a biya ku don kawai ku kwanta a kan gado

Yayin da wadanda zasu yi aiki sa'o'i 37.5 a mako, aikin ba komai bane face kwanciya akan gado.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakanan ana bukatar su gwada katifu daban-daban kowane mako, yin rubutu da kimanta jin dadin su na kwanciya kan katifun.

Manufar aikin shi ne ya taimaka wa kamfanin katifar ya kera katifu wadanda ke ba da mafi kyawun salo ga abokan cinikayya.

Martanin mutane a kafar sada zumunta

@johnny.v23 yace:

"Ina yin haka kowace rana dama. A ina zan nema??"

@soberingmirror

"Kenan zan iya samun kudi saboda bata rayuwata kamar yadda na riga na yi?"

@jamessmithpt

"Kowa ya yi hakan a bara kuma ya kira hakan da kulle."

Wani kamfani zai biya makudan kudade ga mai son ya kalli wasu fina-finai 13

A wani labarin , Akan kalli fina-finai domin nishadi da debe kewa, hakazalika da ma bata lokacin zama ba aikin komai, amma kun taba tunanin akwai fim din da zaku kalla kuma a biya ku kudade?

Kara karanta wannan

Bayan matsalar kwanakin baya, Kamfanin Facebook na shirin sauya suna

Wani kamfanin hada-hadar kudi zai ba da $1,300 (N534,950.00) ga duk wanda ke son zama ya kalli wasu manyan fina-finai masu ban tsoro da aka taba yi a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.