An Yi Rashi: 'Yan Boko Haram Sun Sake Hallaka Babban Kwamanda da Wasu Sojoji a Najeriya

An Yi Rashi: 'Yan Boko Haram Sun Sake Hallaka Babban Kwamanda da Wasu Sojoji a Najeriya

  • Rundunar sojojin Najeriya ta sake yin rashi na dakarunta a hannun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram
  • Tsagerun 'yan ta'addan na Boko Haram sun hallaka wani babban soja yayin wani hari da suka kai a jihar Borno
  • Babban sojan da wasu sojoji sun rasa rayukansu lokacin da suke kan hanyar kai dauki sakamakon harin Boko Haram

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Wani babban jami’in sojojin Najeriya, mai suna Kanar I.A. Muhammad, ya rasa sakamakon wani harin Boko Haram.

Lamarin ya auku ne biyo bayan harin kwanton bauna da ’yan Boko Haram suka kai masa, biyo bayan wani hari da suka kai wa sansanin sojoji a garin Monguno da ke jihar Borno a daren Lahadi.

'Yan Boko Haram sun kashe kwamandan sojoji
Marigayi I.A Muhammad da 'yan Boko Haram suka kashe Hoto: @BrantPhilip
Source: Twitter

Sojojin da ke fagen fama a Arewa maso Gabas suka shaidawa jaridar SaharaReporters hakan a safiyar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

'Yan Boko Haram sun kai hari Borno

Sun bayyana cewa babban jami’in ya rasa ransa yayin da yake jagorantar tawagar kai ɗauki domin fatattakar ’yan ta’addan.

A cewar majiyoyin, ’yan ta'addan bayan sun ƙaddamar da harin ne a daren Lahadi, inda suka farmako wani sansanin sojoji da ke ƙarƙashin bataliya ta 242 a Monguno, wadda ke ƙarƙashin Shiyya ta 3 ta rundunar yaƙi da ta’addanci.

“An kashe daya daga cikin manyan kwamandojinmu, Kanar I.A. Muhammad, a daren jiya lokacin da Boko Haram suka kai hari Monguno. Sun kuma kashe wasu sojoji yayin harin."

- Wata majiya

Yadda aka kashe babban soja

Zagazola Makama ya bayyana cewa bayanai sun nuna cewa a daren 12 ga Afrilu, dakarun Shiyya ta 3 sun fuskanci wani yunƙuri na kutse daga ’yan ta’adda a yankin Charlie 13.

Cikin jarumtaka, sojojin sun fafata da maharan, inda suka tilasta musu guduwa tare da tabbatar da tsaron yankin.

Sakamakon kyakkyawan shugabanci da damuwa da rayuwar mutanensa, Kwamandan ya yanke shawarar ci gaba da tafiya domin ya duba yanayin da ake ciki da kansa.

Kara karanta wannan

Dalilin gwamnan Borno na goyon bayan harin sojin sama duk da rasa rayuka akalla 200

Yayin da yake cikin wannan tafiya ta jarumtaka, motarsa ta taka nakiya (IED) da aka birne a ƙasa, wadda ta kashe shi da sojojinsa guda shida.

'Yan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Rundunar sojoji ta yi jimami

A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar, rundunar ta nuna matuƙar baƙin ciki.

Ta bayyana marigayin a matsayin madubin jarumtaka, sadaukarwa, da kuma kishin ƙasa. Ta ce sadaukarwar da suka yi za ta kasance a zukatan rundunar da kuma ƙasar da suka yi wa hidima cikin mutunci.

Boko Haram ta saki bidiyo

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Boko Haram ta saki bidiyon mutanen da ta kama yayin wani hari da ta kai a Ngoshe da ke jihar Borno.

'Yan ta'addan sun tabbatar da cewa mutanen da suka kama, wanda galibinsu mata ne suna cikin koshin lafiya kuma ba a azabtar da su ko cin zarafinsu ba.

A cikin bidiyon da aka fitar, ƙungiyar ta nuna waɗanda aka sace tare da yi musu tambayoyi kan halin da suke ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng